Connect with us

LABARAI

APC Ta Kafa Kwamitocin Fidda Gwani Na Kujerar Gwamna Ga Kogi Da Bayelsa

Published

on

Jam’iyyar APC a ranar Laraba ta kaddamar da kwamitin da zai jagoranci tantance ‘yan takarar da za su tsaya a zaben fidda gwani na kasance ‘yan takarar gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa. Jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwanin ne a ranar 29 ga watan Agustan nan.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole shi ne ya kaddamar da kwamitina  Abuja, inda ya shawarci kwamitin da su tabbatar sun yi aikin tantancewar yadda ya dace.

Ya ce; yin tantancewar yadda ya dace kawai zai sanya jam’iyyar ba za su rasa ‘yan takarar ba. Rahotanni sun tabbatar da cewa; jam’iyyar APC din sun sanya ranekun 22 da 23 ga watan Agusta a matsayin ranekun tantancewar ‘yan takarar a karkashin jam’iyyar.

Sanata Hope Uzodinma shi ne zai jagoranci membobin mutum bakwai a kwamitin domin tantance masu son tsaya takarar gwamna a Kogi, a yayin da Sanata Abdullahi Gumen zai jagoranci na jihar Bayelsa.

.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: