Connect with us

Nahiyar Afirka

Harin Ta’addanci: An Hallaka Sojojin Burkina Faso 24

Published

on

Rundunar Sojin Burkina Faso ta sanar da cewa adadin sojojin kasar da suka rasa rayukansu yayin harin ta’addanci da wasu ‘yan bindiga suka kai musu ranar Litinin din makon nan ya karu zuwa Sojoji 24.

Harin na ranar Litinin wanda ake dora alhakinsa kan mayakan da ke ikirarin jihadi a yankin Sahel, ya faru ne a yankin Koutoubou da ke arewacin gunduman Soum na kasar Burkina Faso, lokacin da mayakan suka musu kwanton bauna.

A cewar rundunar sojin kasar ta Burkina Faso, baya ga sojojin 24 da suka rasa rayukansu akwai kuma wasu soji bakwai da yanzu haka ke jinya yayin da wasu karin biyar kuma suka batan dabo bayan farmakin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: