Connect with us

TATTAUNAWA

Ministocin Da Buhari Ya Nada Kwararru Ne -Dr. Bature Abdul’azeez

Published

on

Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, Dr. Bature Abdul’azeez ya bayyana cewa ministocin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya zabo ya kuma nada, nagartattun mutane ne wadanda ke da kwarewa a fannoninsu. Dakta Bature ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP A Yau jiya a birnin Kano.

Shugaban ‘yan kasuwar ya ce, wadannan ministoci da a ka nada, za su yi aikin da kowa zai yaba kuma a yi sam-barka. Ya ce, kafin nan da shekarar 2023 Nijeriya za ta koma sabuwa fil.

Ya ce; “Na tabbata tunda Shugaban Kasa ne da kansa ya zabo wadannan ministoci da kansa, kuma duk wanda ya san ba akidarsu ta kishin talaka daya ba, Buhari ba zai dauko shi a matsayin minista ba.”

Haka kuma Dakta Bature Abdul’azeez ya bayar da shawara ga wadannan ministoci kamar haka: “Su wadannan ministoci ina basu shawara da yadda Buhari ya basu amana, toh ya dace su kiyaye amanar, su fid da shugaban kasa kunya don ganin tsare-tsarensa na shirin raya kasa ya kai ga nasara.

“Mai girma Shugaban kasa ya yi shekara hudu, kowa ya ga irin muhimman ayyukan da ya sa su a gaba, wasu an riga an gama da su, wadansu kuma yanzu ake ci gaba da yinsu, wadansu kuma nan gaba za a kirkire su. Lallai matukar wadannan ministoci kowa ya yi aiki tukuru tsakaninsa da Allah da kishin kasa da rike amanar da aka daura masa, na tabbata Nijeriya za ta fita kunyar mara da.

“Abin da ya sa nake wannan jaddadawa da jinjinawa shi ne, ‘yan Nijeriya Allah ya halicce mu a wata irin kasa wacce wadansu da yawa da ake tsammanin masu kishin kasa ne, toh ba masu kishin kasa ba ne. Kuma kasa ce da ba a iya adawa ba, suna makauniyar adawa domin adawar tana sa wa su rika kokarin jefa kasar a cikin bala’i, jefa kasar a bacin suna, jefa kasar a rigingimu da hayaniya. Wannan duk abubuwan da aka yi ta koke-koke da su kaso 90% daga gindin ‘yan adawa ya fito. Kuma kowanne ka taba sai nuna maka shi kwararren dan siyasa ne, kuma dimokradiyya yake goyon baya. Alhali kuma inda a ke goyawa dimokradiyya baya ba haka suke yi ba.

“Su a wadancan kasashen, da zaran an shiga zabe da mutum an kayar da shi, shi kenan zai hakura domin kasarsa ce a gabansa. Amma banda ‘yan adawan Nijeriya, su wani lokacin ma sai ka ji karara a cikin alkaba’I da suke kira ma Shugaban Kasa wani lokacin har da mutuwa da rashin lafiya da kasawa. Sun mance cewa zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya kai labara.” In ji shi.

Shugaban ‘yan kasuwan ya kara nanata cewa: “Buhari wani shugaba ne wanda yake shakka babu a Afrika abu ne mawuyaci ka samu kamarsa, kuma yadda ‘yan adawar Nijeriya suka rufarsa masa ba don mutum ne mai dogaro da Allah ba, kuma ya yarda da kansa ba da tuni zafin adawarsu ya sa ba mu san halin da muke ciki ba a yau.

“Saboda haka hakki ne a kan wadannan sabbin ministoci da su kula, kada Shugaban kasa ya basu amana kuma za su iya ya zama kuma mutum ya koma gefe yana yin uban gida, wanda a sau da yawa idan ba bukatarsu ne ta biya ba, a karshe ta dagule suke fata kowa ma ya rasa.”
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: