Connect with us

LABARAI

Rwanda Da Uganda Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Published

on

A ranar Laraba 21 ga watan Agustan 2019 ne a kasar Angola, Shugabannin kasashen Rwanda da Uganda suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta bada damar kawo karshen zaman tankiyar a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, haka kuma tsoffin aminai da ke ci gaba da zargin yi wa junansu leken asiri, kisan siyasa da kuma katsalandan a harkokin cikin gidan kasashensu.

Bayan saka hannu kan yarjejeniyar a Luanda, Shuwagabanin kasashen Rwanda Paul Kagame da na Uganda Yoweri Museveni, sun dau alkawarin mutunta ‘yancin kasashen juna.

Har wala yau mahukuntan biyu, sun dau aniyar mutunta tsarin da zai samar da zaman lafiya a cikin kasashensu, tare da kaucewa daukar nauyi, da kuma horar da kungiyoyin dake dauke da makamai wajen rikita tsarin zaman lafiyar kasashen na su

Yarjejeniyar dai an rattaba mata hannu ne a gaban shugabanin kasashen ‘Angola, Joao Lourenço, da na jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi, da na dayar Congo, Denis Sassou Nguesso.

Tada jijiyoyin wuya da ake yi tsakanin shugabanin kasashen masu makwabtaka da juna Yuwari Museveni dake kan mulkin Uganda yau da shekaru 33, da Paul Kagame dake kan karaga shekaru 19 da suka gabata, na barazanar tsoma tsama kasashe makwabtansu cikin rikici, tare da haifar da barazana ga tsarin gamayar tattalin arzikin yankin da kuma ci gabansa
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: