Connect with us

RA'AYINMU

Shirin Ruga Da Hadin Kan Nijeriya

Published

on

Babu wani shiri da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi da ya sha maganganun, kamar tsarin kafa Ruga na gwamnatin.

Gwamnatin dai ta fito da shirin ne don kyauta wa sana’ar kiwo zalla ta Fulani Makiya da nufin killace mu su inda za su dinga gudanar da kiwon dabbobinsu maimakon yin yawo barkatai da a ka saba da shi tun tale-tale su na yi. 

Sai dai, an fito da wasu hanyoyin wayarwa da al’ummar da su ke sukar tsarin na Ruga yadda za su fahimci mahimmancin da tsarin ya ke da shi, musamman masu sukar tsarin yadda kowa zai yi na’am da tsarin.

Tsarin na Ruga wata sabuwar hanya ce ta yin kiwon dabbobi a zamance. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya kamata gwamnatin tarayya ta cigaba da yunkurinta na  tsarin na Ruga ko kuwa ta yi watsi da shirin?

Dalilin wannan tambayar shi ne, yadda wasu sassan Najeriya su ka dinga tayar da jijiyar wuya da kuma yin kumfar baki a kan tsarin, inda su ke ganin gwamnatin tarayya, ta na da wata manufa da ta ke boyewa dangane da tsarin na Ruga, inda hakan ya janyo cigaba da yin mummnar suka a kan tsarin.

Abin mamaki ga tsarin na Ruga, mun fara  jin tsarin, wata hanya ce ta killace Fulani Makiya a guri guda, don gudanar da kiwonsu da kuma gudanar da sauran kiwon dabbobinsu, inda kuma hakan zai taimaka wa Nijeriya wajen yin dogaro a kan kokarin farfado da aikin noma a kasar, inda idan har an wanzar da tsarin, zai taimaka wajen fitar da amfanin goma zuwa kasashen ketare har kuma tsarin ya iya taimakawa wajen wadatar da bukatun kimanin al’ummar kasar miliyan 190.

LEADERSHIP A YAU, a nata ra’ayin fito da tsarin, ya zama wajibi a jinjinawa gwamnatin  shugaban kasa  Muhammadu Buhari BISA ganin cewa, tsarin zai  taimaka wajen cika burin kudurin gwamnatinsa na alkawarin da ya yi na  tsamo Nijeriya daga cikin kangin talauci a cikin sauri. Tsarin Ruga ko kuma yin kiwo a karkara, an shigo da shi ne daga yankin Euro a lokacin Turawan mulkin mallaka.

Wani tsari ne na killace dabbobi don yin kiwonsu a guri guda idan aka kwatanta da irin wajen yin kiwo da aka killace na  Obudu akwai kuma makamanin irin wannan tsarin na Ruga a cikin Nijeriya  da ake yinsa a saukake a nahiyar Euro da turawan mulkin mallaka suka kirkiro dashi.

Bugu da kari, tsarin na Ruga an san shi sosai a lokacin jamhuriyya ta biyi a kasar nan

Shin, tsarin ya bace ne saboda yadda alumma suka kara yin ya wa a kasar nan domin ko a cikin tasawirar kasar nan, akwai ida suka nuna an ware guraren yin kiwon dabbobi ga Fulani Makiya dake kasar nan?

Har ila yau, tsarin na Ruga  a lokacin gwamnatin shiyya na kasar nan, daidai yake da na gonar  Ulonna da aka kebe don yin kiwo, inda a wancan lokacin, tsarin ya taimakawa yankin da yakin basa na Biafra har zuwa watanni uku.

Bugu da kari, a uankin Arewacin kasar nan kuwa, tsarin na Ruga sananne ne domin kuwa, kamar a jihar Biniwe an san shi sosai.

A ya yin da tsarin dalar Gyada na da yake yin tashe,ya taimaka matuka wajen fitar da kaya zuwa kasashen ketare harda sarrafa  Aufuga.

Yankin Kudu maso Gabas kuwa, suma suna da irin nasu tsarin na gudanar da jiwon dabbobi da kuma cocoa wanda sukafi yawan fitar dashi zuwa kasashen ketare don samun kudin shiga.

Sai dai, gudanar da tsarin yana da kamar wuya, idan a ka yi la’akari da irin banbancin yare da kabulu da kasar nan take da su.

Sai dai, a lokacin da gwambatin da kuma tsarin nata, an tsara za a gudanar da tsarin ne a daukacin fadin kasar. Wadanna jihohin sun hadada, jihohin dake cikin  Yankin Middle-belt, inda guda uku su ka hadada, jihohin dake cikin yanjin Arewa Maso Gabas da kuma jihohi biyu dake a yankin Arewa maso Yamma.

A yankin Arewa maso Yamma akwai jihohin  Kebbi, Sokoto, inda kuma akwai Arewa maso Gabas da suka hada da  Borno, Bauchi da kuma  Yobe. Turawan mulkin mallaka ne suka kikiro da shirin a shekarar 1856 a kasar nan don a habaka kiwo a kasar. A ra’ayinmu, wannan labarai ne mai kyau kuma za’a amfana da shi.

Muna ganin ya kamata a bibiyi tsarin na Ruga sai an kai makurarsa. Aikin na tsarin Ruga,doke a kara jaddada mahimmancin da yake dashi, nusamman ga jihohin kksar nan da suke da nufin wanzar da shi a jihohinsu.

Mun juma yi amanna cewa, tsarin na Ruga zai taimaka wajen samar da  ayyukan yi ga yan kasar nan, musamman matasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: