Connect with us

RAHOTANNI

An Nemi ‘Yan Nijeriya Su Rika Addu’ar Samun Kwanciyar Hankali Ga Kasa

Published

on

Shugaban masu sana’ar sayar da goro na Afirka Garba Ba’are, ya yi kira ‘yan Nijeriyaa da su zauna lafiya da junansu. Garba Ba’are ya yi wannan kira ne a yayin tattaunawarsa da wakilin LEADERSHIP A Yau Juma’a. “ Zaman lafiya a Nijeriya, shi ne abin da ya kamata ‘yan Nijeria su yi don ganin an sami ci gaba a wannan Kasa, yawan zage-zage da yawan fadace-fadace ba shi ne zai warware matsalarmu ba, saboda haka ya kara da cewa wannan al’amari na ci gaban Nijeriya abu ne wanda da ya shafi kowa ya ba da gudumawarsa ba wai a dogara da Shugaban Kasa shi ke da laifin komai ba ko alhakin komai ba.

Hakki ne na duk ‘yan Nijeriya mai kishin Kasarsa, saboda haka ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su taimaka wa Shugaban Kasa da addu’a da kokari da irin aiki da yasa agaba na ci gaba domin ga Kasa ta bun bunkasa, shugaban masu goro na afrika Alhaji Garba Ba’are ya kara da cewa yau fa lokaci ya yi da duk yan najeriya kowa zai farka daga barci, da nema ya ci ban za yaci bulus shi ne abin, da kowa ya ke so ya samu lokaci ya yi, da kowa zai farka da gani kowa zai yi cudan ya da gani ya samin amfani da dukkanin wannan Kasa, da cigabanta, Shugaban Alhaji Garba Ba’are ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammad Buhari da irin kokari da yake na gani Kasa ta bunkasa da ci gaba da tartalin arziki Kasa, Shugaban Garba Ba’are Shugaban masu goro na africa ya yaba da kyakyawa ayyuka da ya sa a gaba musanman ganin yadda yake kokarin hada Kasashen Africa da kuma duniya baki daya domin a fahimci al’amarin da aka sa a gaba Kasar.

Shugaba Garba Ba’are ya godewa Shugaban Kasa da kokarin da yake na samar da zaman lafiya da hadin kai a wannan Kasa, saboda haka ya yi kira ga duk dan Nijeriya shi ma ya ta shi tsaye gani ba shi gudunmawar iya daidai gwargwado musanman kuma Shugabanni da ministoci don Allah su yi tsayin daka su rike wannan amana da aka danka musu ganin an samu ci gaba a wannan Kasa, a bangare ‘yan Arewa mazauna legas da su ta shi tsaye su rike kansu su taimaka wa junansu da kuma shiryawa kansu zaman lafiya ba yawan goratawa juna ba asali go tsarin rayuwa ba wannan al’amari abu ne wanda yasha fi kowa domin kowa ya ba da gudumawarsa a Kasa domin ganin Nijeriya ta samu ci gaba, a karshe Shugaban Garba Ba’are ya yabawa Gwamnan Legas baba tunde saolu da irin kokari da yake a wannan jiiJiha tamu ta legas, kuma yana fata Allah ya sa wannan ci gaba da a kasa Allah ya sa ya zama alfahari a gare mu da kuma Nijeria baki daya yana wa Nijeriya fatan adu’a Allah ya zauna da mu lafiya  Allah ya ciyar da mu gaba da fatan alkairi amin .
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: