Connect with us

FITATTUN MATA

Jaruman Matan Da Ke Cikin Sabbin Ministocin Buhari Da Ma’aikatunsu

Published

on

A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ministoci mata su bakwai (7) daga cikin Ministoci 43 da ya nada a zangonsa na biyu.

Jaruman Matan an rantsar da sune tare da sauran takwarorinsu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ministoci guda bakwai da suka kasance jarumai a wannan lokacin da kuma jerin ma’aikatun da aka turasu sun hada da:

Hajiya Sadiya Umar-Farouk Minista a ma’aikatar harkokin da suka shafi bayar da tallafi da agaji da kuma magance  bala’i ko ibtila’i.

Hajiya Maryam Katagun, karamar Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari.

Sanata Gbemisola Saraki, karamar Ministan Sufuri.

Sharon Ikeazu, karamar Ministan Muhalli.

Hajiya Zainab Ahmed, Ministan Kudi, Kasafi da tsare-tsare na kasa.

Dame Pauline Tallen, Ministan harkokin mata da bunkasa walwalar al’umma.

Ita kuwa, Rahmatu Tijjani aka tura karamar Ministan babban Birnin tarayya FCT, Abuja.

Filin Fitattun Mata na jaridar Leadership A Yau Juma’a, zai kawo muku cikakken tarihin kowanne daga cikin jaruman mata Ministocin Buhari a kowace ranar Juma’a idan kuna biye da mu. Amma kafin nan, ga somin tabin tarihinsu, za mu kawo cikakken tarihon kowanne daga cikinsu domin ku sansu sosai.

1. Sadiya Umar-Farouk, ta fito daga jihar Zamfara.

Sadiya Umar Farouk gabanin ta zama Minista ita ce shugabar hukumar ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira.

Tana da digiri a Gudanar da harkar Kasuwanci daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria a jihar Kaduna da kuma digiri na biyu a harkokin kasasehn waje da Diflomasiyya duk daga wannan jami’ar, daga ranar Larabar da ta wuce ta zama sabowar Minista a ma’aikatar harkokin da suka shafi bayar da tallafi da agaji da kuma magance  bala’i ko ibtila’i.

2.  Maryam Yalwaji Katagum, daga jihar Bauchi.

Maryam Yalwaji Katagum gabanin ta zama Minsita a Nijeriya ta kasance zaunanniyar jakadiyar Nijeriya a hukumar UNESCO tun watan Yunin 2009.

Tana da Digiri na farko da na biyu da sauran karatun da ta yi, ta kasance Minista ne daga jihar Bauchi inda suka kasance tare da Malam Adamu Adamu. Maryam dai yanzu haka ita ce karamar Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari.

3. Gbemisola Saraki (Kwara)

Gbemisola Saraki tsohuwar sanata ce da ta wakilci yankin Kwara ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya, sannan ta kasance ‘yar uwar tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki.

Ta yi digirinta na farko a Jami’ar Sussed da ke Birtaniya inda ta karanci Tattalin arziki da sauran takardun shaida da ta mallaka na karatu. Yanzu haka ita ce karamar Ministan Sufuri a Nijeriya.

4.  Sharon Ikeazu, Buhari ya zabeta Minista ce daga jihar Anambra.

Sharon Ikeazu gabanin ta zama Ministan Muhalli a Nijeriya ita ce shugabar hukumar fanshon ma’aikatan gwamnati (PTAD) wacce Shugaba Buhari ya nada ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

Rahotanni sun ce a shekararta ta farko a ofis, ta gabatar da tsare-tsare da dama da suka kawo sauyi a hukumar ta PTAD.

Tana da digiri a fannin shari’a daga Jami’ar Benin da kuma takardar shaidar kammala makarantar koyon shari’a a 1985, ta zama karamar Ministan Muhalli a Nijeriya ne bayan da shugaban kasa Buhari ya zabeta kana aka tantanceta.

5.  Hajiya Zainab Ahmed, daga jihar Kaduna

Zainab Ahmed ce tsohuwar ministar kudi a karo na farko na mulkin shugaba Buhari na 2015, inda aka nada ta a watan Satumbar 2018 bayan da Kemi Adeosun ta yi murabus.

Zainab tana da digiri a karatun Akanta da digiri na biyu a Gudanar da Harkar Kasuwanci. Yanzu haka ita ce Ministan Kudi, Kasafi da tsare-tsare na kasa, ana ganin muhallin da Buhari ya bata ya dace sosai da ita, ganin cewar tana da kwarewa sosai kan hada-hadar kudi na tsaron shekaru 28.

6.  Dame Pauline Tallen, wacce Buhari ya zabo daga Filato

Pauline Tallen tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar Filato ne a 2007 kuma mace ta farko da ta rike wannan mukamin a arewacin Nijeriya.

A shekarar 1999 ta zamo ministar kimiyya da fasaha a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Ta kuma taba yin takarar zama gwamnar Filato a 2011 amma sai Jonah Jang ya kayar da ita. Yanzu kuma ta zama sabowar Ministan harkokin mata da bunkasa walwalar al’umma.

7. Ramatu Tijani wacce aka zabo daga jihar Kogi.

Ramatu Tijani jawurtacciyar ‘yar jam’iyyar APC, ta halarci Jami’ar Ahmadu Bello Zariya inda ta karanci fannin Tsara birane.

Ta yi digiri na biyu a Sha’anin Mulki, tana karatun digirin-digirgir dinta a fannin tsaro a wannan ABU din.Yanzu haka Rahmatu Tijjani ita ce karamar Ministan babban Birnin tarayya FCT, Abuja.

Filin Fitattun mata zai kawo muku cikakken tarihin rayuwarsu daya bayan daya. Za ku iya aiko da sakonni dangane da wadannan jaruman kai tsaye ga wannan filin a kidrisdoya200@gmail.com ko a tuntubi 07069724750
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: