Connect with us

WASANNI

Rivaldo Ya Zargi Messi Da Kawo Wa Coutinho Kancal A Barcelona

Published

on

Tsohon dan wasan Barcelona Rivaldo ya zargin kaftin din kungiyar na yanzu, Lionel Messi, da taka rawa wajen haddasa rashin nasarar Philippe Coutinho a kungiyar.

A watan Janairu na shekarar 2018, Coutinho ya koma Barcelona daga Liverpool kan Yuro miliyan 148, sai dai har yanzu, jagororin kungiyar Barcelona ba su gamsu da kwazon dan wasan ba.

Rashin taka rawar ganin Coutinho ya sa a halin yanzu ya koma kungiyar Bayern Munich tsawon shekara 1 a matsayin aro, kan Yuro miliyan 8.5, da kuma zabin komawa kungiyar dindindin kan Yuro miliyan 120.

Yayin tsokaci kan halin da Coutinho ya tsinci kansa, Rivaldo, tsohon tauraron Barcelona, ya ce mamaye al’amuran da Messi ya yi ba tare da bai wa Coutinho dama ba shi ne ya haddasa gazawar da dan wasan ya yi wajen cika burin ganin ya maye gurbin tsohon kaftin din kungiyar ta Barcelona, Andres Iniesta.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: