Connect with us

WASANNI

Tsohon Dan Wasan Ghana Junior Agogo Ya Rasu

Published

on

Tsohon dan wasan Ghana wanda ya taka leda a Nottingham Forest da Bristol Rovers, wato Junior Agogo ya yi ban kwana da duniya yana da shekaru 40. A shekarar 2015, Agogo ya gamu da cutar shanyewar barin jiki, rashin lafiyar da ta kai shi ga fuskantar kalubalen furta magana.

Tuni tsoffin kungiyoyin da ya taka leda suka mika sakonnin ta’aziyar rasuwarsa. Agogo wanda ya fara taka leda a Sheffield, ya buga wa kasarsa ta Ghana wasanni 27, yayin da ya ci mata kwallo 12.

Magoya bayansa za su ci gaba da tuna shi musamman kan kwallaye ukun da ya zura a ragar Nijeriya a wasan da kasashen biyu suka buga a gasar Cin Kofin Kasshen Afrika a shekarar 2008 a birnin Accra, abin da ya bai wa Ghana nasara a wancan lokaci.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: