Connect with us

SIYASA

Gwamnan Neja Ya Umurci A Yi Gyaran Ofisoshin Ma’aikatan Gwamnati

Published

on

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya umurci ma’aikatar ayyuka da ci gaban kasa ta jiha da ta tabbatar ta yi gyare-gyaren ma’aikatun gwamnatin jihar domin samar da kyakkyawan wuraren ayyuka ga ma’aikatan jihar

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kaiwa sakatariyar ma’aikatar cigaban matasa ta jihar da hukumar kula da hasken wutan lantarki ( NSREB) da ofishin sakataren gwamnatin jiha da ke minna.

Gwamnan ya nuna damuwarsa akan yadda ya ga halin da ma’aikatun gwamnati ke ciki, inda ya nuna bukatar kammala ayyukan gine-ginen da ke cikin harabar ma’aikatan. Yace dukkanin ma’aikata akwai bukatar samar masu kayan aiki duk yadda ma’aikacin gwamnati yake ta yadda zasu dauki aikinsu da muhimmanci dan samar da abinda zai kawo wa gwamnati cigaba.

“ Ya ce wasu ofisoshin na bukatar gyara, tare da gina sabbi ta yadda ma’aikata za su ji dadin gudanar da aiki. Wannan zai ba su kwarin guiwar yin aiki bisa kwazo da jajircewa dan samun gudanar da aikin gwamnati yadda ya dace.,”

Gwamnan ya umurci ma’aikatar ayyuka ta jiha da ta kammala ayyukan da aka faro ba a kammala ba, da kuma gyaran ma’aikatun da suka lalace a dukkanin ma’aikatun gwamnatin jiha.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: