Connect with us

SHARHI

Me Ya Sa Har Yanzu Boko Haram Ke Ci Gaba Da Zama Barazana A Jihar Borno

Published

on

  A ‘yan kawanakin nan ne kungiyar Boko Haram ta cika shekaru 10, tana gudanar da kai hare-hare da makamai, wadda ta fara bayan kashe shugaban ta, Malam Muhammad Yusuf, a jihar Borno, inda ta bazu zuwa Arewa-maso-gabas da ma wasu sassan Arewaci da wasu bangarorin Nijeriya.

Matsalar tabarbarewar tsaron da ta biyo bayan wannan bahallatsar ta jawo asarar dubun-dubatar rayukan jama’a da tilasta wa miliyoyi kauracewa yankunansu tare da asarar dimbin dukiyoyin da Allah ne kadai ya bar wa kansa sanin yawansu- baya ga jefa tsoro da fargaba da ya jawo wasu fadawa matsalar tabin hankali da wargajewar notunan tunani.

Rahotanin da gwamnatoci ke bayar wa tare da na kungiyoyin bayar da jinkai, a yankin arewa maso gabas sun bayyana cewa matsalar ta jefa dubun-dubatar kananan yara cikin maraici da adadi mai yawa na mata wadanda suka koma zawarawa, barkewar cutuka tare da matsalolin rayuwa a wannan yankin.

Tun bayan ‘yan lokuta kadan da faruwar matsalar, gwamnatin tarayya ta sha daukar alkawurran dakile kaifin ‘yan kungiyar Boko Haram. Lamarin tabarbarewar tsaron ta jawo cece-kuce tare da nuna wa juna yatsa; tsakanin wasu gwamnatocin jihohi da ta tsakiya (musamman lokacin tsohuwar gwamnatin PDP). Wani sa’ilin kuma ta kaure tsakanin jami’an tsaro ko da yan kasa dangane da matakan yaki da matsalar.

Masana sun yi ta tofa albarkacin bakin su dangane da wannan matsala mai kama da fatalwa; yau a ce an murkushe Boko Haram, gobe ka ji sun kai hari can…duk da ko yadda masu nazari kan bayar da shawara, kan cewa a bi a hankali tare da yin aiki a tsanake- saboda yaki da Boko Haram ba yaki ne na gaba-da-gaba ba, fada ne irin na sunkuru, wanda ba kasafai ake cin galabarsa a dan kankanen lokaci ba.

Kamar yadda masana a harkar tsaro tare da bibiyar aikace-aikacen wannan kungiya ta Boko Haram, sun bayyana yadda kungiyar ta rabu kashi-kashi, wala-alla wata sabuwar dabarar yaki ce don raba hankalin jami’an tsaro da gwamnati.

A baya-bayan nan, kungiyar Boko Haram, a karkashin reshen Islamic State in West Africa Probince (ISWAP), sun yi kwamba tare da kai wani mummunan hari a garuruwan Gubio da Magumeri.

Bayanai daga yankin, sun bayyana yadda daruruwan maharan suka kai wannan farmakin, wanda suka cinna wa gidajen jama’a wuta tare da makarantu da muhimman wurare da wawushe kayan abinci da na masarufi. Mayakan basu tsaya nan ba, sun halaka wani dan ‘Cibilian JTF’, kamar yadda wata majiya ta labarta mana. Al’amarin da ya tilasta wa daruruwan jama’a arcewa daga wadannan yankuna- da suka kunshi mata da kananan yara.

Da yake bayar da tabbacin afkuwar kai harin, shugaban riko a karamar hukumar Gubio, Hon. Zanna Modu Gubio ya bayyana cewa, maharan Boko Haram din sun kai harin a garin da kimanin karfe shida da rabi na yamma (6:30 pm), a lokacin da jama’ar musulmi ke gudanar da sallar magariba, wanda kan ka ce kwabo, suka bude wa jama’a wuta ba kakkauta wa tare da kona gidajen jama’a da dukiyoyin su.

Ya ce, “Wannan abin bakin-ciki ne inda yau mako guda da kai wani mummunan hari a garin Gubio, lamarin da ya jawo janyewar sojoji daga yankin, wadanda aka canja musu wajen aiki, sannan kuma gashi yanzu wasu mayakan sun sake kai wani harin da misalin karfe 6:30 na yamma, a daidai lokacin da jama’ar Gubio ke gudanar da sallar magariba a masallatai, harin da ya rutsa da dimbin jama’ar da ba su san hawa ba balle sauka tare da kona gidajen jama’a da dukiyoyi maras adadi”.

“Wanda a halin da ake ciki yanzu (a lokacin da aka kai wannan harin) ina Maiduguri wajen halartar bikin rantsar da sabbin kwamishinoni, kwatsam muka samu labarin wannan, mun kadu matuka, daga nan sai na rika samun kira ta ko’ina kan cewa maharan Boko Haram sun kawo hari a Gubio”.

Ta nasu bangaren, sojojin Nijeriya a karkashin rundunar Lafiya Dole, inda ta yi karin haske dangane da rahotanin da wasu kafofin yada labarai ke bayar wa, kan harin da maharan Boko Haram suka kai, ranar Laraba, a garin Gubio da Magumeri da ke jihar Borno.

Bayanin wanda ya fito daga bakin babban jami’in hulda da jama’a, na rundunar Lafiya Dole da ke yankin arewa maso gabashin Nijeriya, Kanal Ado Isa, a cikin sanarwar ya bayyana cewa, kawai wannan harin ya rutsa da yan ‘Cibilian JTF’, ta hanyar musayar wuta tsakanin su da mayakan.

Ya kara da cewa, wadannan hare-haren da yan kungiyar Boko Haram suka kai, sun kitsa shi tare da auna mazaunin sojojin ne, don samun damar kai ga shagunan yan kasuwa don su saci kayan abinci, su arce da su.

Kanal Isa ya ce,  “Rahotanin da kafafen yada labaari daban-daban ke yada wa dangane da wannan hari wanda mayakan Boko Haram suka kai a garuruwan Gubio da Magumeri; ranar Laraba, ta 21 ga watan Agusta, shi ne ya ja hankalin rundunar Lafiya Dole”.

“Saboda kaucewa rudani, da harzuka zukatan jama’a, rundunar Lafiya Dole, ta ga ya dace ta yi karin haske dangane da wannan harin, wanda mayakan suka kitsa shi da nufin abka wa sojojin Nijeriya, wanda hakan zai basu dama wajen fantsama a shagunan yan kasuwa dake garuruwan don su yi wasoson kayan abinci da na masarufi”.

“A hannu guda kuma, sojojin Nijeriya sun mayar wa maharan Boko Haram din zazzafan martani”. In ji shi.

“Ta sakamakon haka ne, ta hanyar musayar wuta, ya tilasta dole maharan suka saduda, suka arce daga garin, lamarin da ya jawo; a kokarin su na gudowa, ya jawo hakan ya shafi wasu gine-gine wadanda suke a kan hanyar- sa’ilin da suke gudun”.

“Duk da wannan kuma, babu wani sojan da ya gamu da ajalin sa balle ko lalata wasu makaman sojoji, sabanin labaran da ake bayar wa a kafafen yada labarai. Har wala yau kuma, amma akwai ‘Cibilian JTF’ guda daya wanda ya rasa ran sa- a lokacin musayar wutar, kana da karin wasu wadanda suka gamu da mabambantan raunuka”.

“Sannan kuma, a halin da ake ciki yanzu, jami’an tsaro sun dawo da doka da oda a yankin, inda tuni jama’ar suka ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum, kamar yadda suka saba”.

“A hannu guda kuma, rundunar sojojin Nijeriya tana kara kira ga jama’a da cewa su ci gaba da bai wa rundunar sojoji tare da sauran jami’an tsaro da ke aikin a wannan yanki, cikakken goyon baya da hadin kai tare da bayar da labarin duk wani bata-gari don daukar matakin da ya dace”. In ji shi.

A hannu guda kuma, wasu majiyoyi sun bayyana cewa, wadannan hare-hare na mayakan Boko Haram ya shafi ilahirin kananan hukumomi 10 da ke arewacin jihar Borno. Yayin da shugabanin al’ummu a yankin suka bayyana cewa akwai dandazon yan Boko Haram masu yawan gaske a kananan hukumomin Abadam, Kukawa, Guzamala, Nganzai, Marte, Magumeri Gubio.

Sun bayyana cewa, “Baka yi kaharu ba idan ka ce mayakan su ke iko da kashi 70 cikin dari na wadannan yankunan da na zayyana maka. Kuma wuraren da kadai za ka iske sojoji su ne Mobbar, Monguno da Kaga, hakan ya ba mayakan Boko Haram damar kai-komo inda suke so a yankin”.

Shi ma wani shugaban al’ummar ya sake bayyana cewa, za ka samu mayakan da ke biyyaya ga Shekau sun fi zama a  yankin dajin Sambisa, Bama, Konduga, Damboa, Gwoza, da wani yankin Chibok da sauran su.

“Wanda hakan ya nuna kan cewa ko dai maharan Boko Haram su ke rike da kaso mai yawa na kananan hukumomin ko da ko ko ba su rike da shalkwatar su”. In ji shi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: