Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (57)

Published

on

Ko da Hamdiyatul’aini ta doshi lambun gashi nan gabanta tana kara tunkarar sa, sa rika jin wadansu irin sautika kamar na tsuntsaye, wani abin kuma kama da gurnanin zaki, haka dai kamar kukan wani abu ta ba ta taba saninsa ba har ta isa daura da kofar lambun.

Sai ta ji motsi babba kamar za a fito daga wurin, jin haka sai zare takobinta ta zauna cikin shiri, gama zare takobin ke da wuya sai ga wani kutunkun bauna ya keto ta jikin danger lambun kamar dai mahaukaci ne, bai ma ganta bay a tinkari wata kasaitacciyar bishiya, da zuwa ya sa kaho ya kwashi bishiyar na sama, Hamdiyatul’aini ta duba ta ga a duk warin babu wata itaciya mai girman bishiyar nan amma bugu daya ya yunbuke ta daga cikin kasa har jijiyarta babu abin da ya yi saura.

Dokin ya razana yayi wata irin haniniya yayi rimi kamar za su fadi ta rike shi, a nan sai ta tuna da dabarar da aka koya mata a yayin koyon yaki cewa, a duk sanda ta ga irin haka, to ta sakko daga kan dokin gudun kada wannan dabbar ta hallaka mata doki.

Nan da nan ta sakko daga dokin, ko da namijin baunar nan ya jiyo haniniyar doki sai ya juyo ya nufo wurinsu haikan, bakinsa yana fitar da wani irin bakin hayaki mai zafi, ta yi sauri ta kauce daga muhallin da dokin yake, ganin haka shi kuma sai zaton ko guduwa za ta yi, don haka sai ya bita cikin wannan hali na hauka, da zuwansa ya tasam mata da nufin ya diro kanta, sai mirgina a kasa wurin wucewarsa sai ta sare kafafunsa na gaba, ya fadi can kafin yunkurinsa na biyu ta haye da sara a kansa tun yana iya yunkuri har ya daina.

Daga nan fa ta fusata, ta jowo dokin nata zuwa inuwar wata bishiya ta ajiye shi, tunkari kofar lambun kai ka ce, gidanta za ta shiga, an yi shirin wasu kofofi na ciyawa kayatattu, ta wuce kofar farko lafiya babu abin da ta gani, haka zalika kofa ta biyu da ta uku,  A kofa ta uku wadda kuma ita ce karshen da zaka shiga farfajiyar lambun nan ta yi arba da bakin kumurci, wanda yana jin shigowarta ya mike tsaye a kan jelarsa ya fasa kai, amaimakon idan yayi tsartuwa ta ga yawunsa ya fito sai ta ga wasu kananan macizan sun fito nan take sun girma, idan kuma sare su sai ta ga bayan sun kwanta sais u tashi, a nan ta gane duk na sihiri ne babu abin da za su iya yo mata, shi kuwa babban jifansa ta yi da takobi ta tsinka shi biyu.

To wurin zuwa dakar takobin ne kuma ta sunkuya za ta dauka sai wani gawurtaccen gwaggon biri ya diro mata baya, ya yi jifa da ita can gefe, ta zaro kibiya ta sanya a kwari ta harbe shi ta ga caraf ya rike kibiyar, a karo na biyu ta sake harbinsa ya sake rike kibiyar, ta yi sauri ta tashi tsaye, a nan sai ta sake tuna wata dabarar, ko da ta sake ciro wata kibiyar sai ta yi tofin bisimillah a jiki, da ta harba ya kama sai ya yi bindiga ta yi sauri ta tsince kibiyoyinta ta kuma dauki takobinta.

Jin karar bindigar nan ya sa dukkan wasu halittu da suke cikin wurin sun yunkuro domin kawo dauki, sai ta samu cikin duhuwar danger lambun ta buya domin ta ga irin halittun da kuma adadinsu. Sai ta ga cikin dabbar da fi ko wacce karfi shi ne wani jan zaki da ya fito yana kan gaba suna biye da shi, sai kuma wata damisa da kuraye biyu, sauran daga dawisu sai wadansu irin tsuntsaye na sihiri.

Zakin ya zo ya kwanta yana fuskantar inda take, “ Bisa dukkan alamu fa zakin nan ya fahimci ina cikin wurin a boye,” ta fada a zuciyarta. Sauran dabbobin kuma suka yi wucewa zuwa waje ya zama saura zakin, da ta fusata ta yi wata irn fita kafin ya mike ta cake shi da wani itace mai dafi da tsini, ya yunkura ya mike kafin wani yunkurin ta yi masa kaca-kaca da takobi.

Sai ta yi tunanin kada wadan can halittun su shiga gari su fara hallaka mutane, tan agama tunaninsu sai ta ji dawowarsu, ta koma bayan wata itaciya, ta sanya kibiya ta dirka wa daisar nan, ita ma ta fadi nan a mace da hakan nan ta kashe kura, ragowar kuma ta bisu da takobi ta hallaka su.

Daga nan ta ji shiru kamar babu kowa a lambu, sai ta shiga har ainihin muhallin da shi bokan yake,ta same shi kwance bisa fatar wata bakar dabba, ta ce, “ Ni ce sarauniya Hamdiyatul’ani na kammala da duk wani abu da kake takama da shi daga kan na sihiri zuwa na gaske saura kai, shin za mu shata filin daga da kai ne ko kuwa kana da wasu halittun da za su fada da ni, ga ni yau a gabanka?”

Boka Nammamu ya cira kai ya ce, “ Ba ni da wani tasiri a yanzu, amma dai na san ko da kin hallaka ni ke ma kina daf da hallaka, domin Aswadu dan Sauda’u mai daukar fansa, kuma duk abin da kika yi a nan labari ya ishe shi. yarinya ki yi ta kanki, domin ni dama labari ya isar min cikin bincike, cewa ke ce ajalina, amma dai nay i imanin Aswadu zai daukar min fansa.

Hamdiyatul’aini ta yi tsaki ta ce, ba z aka iya komai ba, har na tsaya ina neman bayanai? Ta tsinke kansa da takobi ta fito ta haye dokinta ta dawo daf da sallar magriba/ tana zuwa wurin masu tsaron Ksar da suke tare da mutanenta suka ganta jikinta duk jini, daya daga cikin masu tsaron Kasar nay a tambaye me ya faru? Ya rufe bakinsa sai suka ga lambun ya yi bindiga, ta ce to ga amsar tambayarka can, yanzu dai muna kan hanyarmu ta isa gidan sarki ko a daren yau ko a wayewar garin gobe idan muna da sauran numfashi cikin yardarm Allah zai tafi lahira.

“ To tunda na fahimci ke macece kuma Musulma ce, ki zauna nan mu yi Sallar magriba tare, yau ran ace mai matukar muhimmaci a garemu, sua nuna mata wuri ta yi wanka ta sauya kaya suka yi Sallah. Can bayan Sallah isha’i sai suka hango feshin wuta, ta tambaye su dalilin haka, suka ce hakan yana alamtawa sarki da jama’ar gari cewa akwai mummunan al’amari da zai faru ko ya faru a yau zuwa gobe, mun sani kabari ya same shin a wannan fadan da kika yi, ba don haka ba muna nan za ki gay a zo ya wuce da rkumi zuwa wurin boka shi zai gaya masa abin zai faru, domin jiya haka nan ya zo ya wuce da shi ashe al’amarin zuwanki zai bas hi labari.

Daya daga ciknsu ya ce, “ Amma bisa shawara ‘yata, ya kyautu a ce kin bari zuwa wayewar gari kowa yana gani ki kashe mana azzalumin sarkin nan kuma ya zama ke zaki mulki wannan Kasa mai ni’imah, amma kafin haka bari mu kawo maku abinci” ya aika aka kawo masu nau’in abincin da suke so, dare ya yi suka ba ta wurin kwana suka ci gada da gadinta zuwa wayewar gari. 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!