Connect with us

LABARAI

Gwamna Zulum Ga Sabbin Kwamishinoni: Kowa Ya Tsaya Ma’aikatarsa, Bama Son Yawan Zirga-zirga Gidan Gwamnati

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ja kunen sabbin kwamishinonin jihar cewa ba zai lamunta da yawan kai-komon su zuwa gidan gwamnati ba, kowanen su ya tsaya ma’aikatar da aka tura shi ya yi aiki, face sai da gayyata ki idan wani muhimmin lamari na gaggawa ta taso.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a jawabin sa wajen rantsuwar da sabbin kwamishinonin su 22 tare da masu bashi shawara, mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda babban Jojin jihar Mai Shari’a Kashim Zannah ya jagoranta a ofishin mataimakin Gwamnan jihar.

“Saboda haka kowanen ku ya zauna ma’aikatar da aka tura shi; ya gudanar da aikin sa, ba ma son yawan zirga-zirgar zuwa gidan gwamnati barkatai, face idan an gayyato ka ko wani lamari na gaggawa”. In ji Zulum.

Bugu da kari kuma ya kalubalanci sabbin kwamishinonin da cewa su tashi tsaye don yin aiki tukuru; ba ji ba gani, da sadaukarwa wajen samun tabbacin cimma kyawawan manufofin da ingantattun tsare-tsaren gwamnatin sa.

A hannu guda kuma, Gwamna Babagana ya kurkiro da sabuwar ma’aikatar kimiyya da fasaha a jihar, don samun sauki wajen farfado da ci gaban tattalin arzikin jihar ta hanyar amfani da hanyoyin kimiyya na zamani wajen zaburarwa da tanadin abubuwan da jihar ke samar wa tare da saukaka aikin gwamnati na yau da kullum.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!