Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnan Bauchi Ya Aza Tubalin Shinfidar Hanya Mai Nisan Kilomita 58

Published

on

A jiya Asabar ne gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya kaddamar hadi da Aza-tubalin fara gina sabon titi mai nisan kilomita hamsin da takwas (58) da za a shimfida wanda zai hade kananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa.

Yankunan da za su mori wannan sabon aikin da za a yi musu sun hada da yankin Yalwan Duguri, Badaran Dutse, Birim, Bajama, Kumbala, Kundak, Wurno da kuma yankin Burga da ke karamar hukumar Tafawa Balewa da Kuma Alkaleri.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin a kauyen Burga, gwamnan jihar na Bauchi, Bala Muhammad, ya shaida cewar an amince da baiwa kamfanin TRIACTA Nigeria Limited damar gudanar da wannan aikin ne kan kudi sama da naira biliyan takwas (8b) wanda ake fatan kammalawa nan da shekaru biyu masu zuwa.

Ya kuma ce, yanzu hakan, tunin gwamnantin jihar ta biya naira biliyan hudu ga kamfanin da zai gudanar da wannan aikin domin samun damar gudanarwa a kan lokaci don jama’an da aka yi dominsu su fara amfana.

A cewarshi, bayar da wannan aikin, yana daga cikin tsare-tsare da shirye-shiryen da gwamnatinsa ta zo jihar da su, yana mai fadin cewar kyautata rayuwar jama’an jihar ta fuskacin samar musu da ababen more rayuwa, gina musu muhallai, shinfida tituna da kyawawan aiyukan tsara birane da karkara ne ya sanya a gaba a daidai wannan lokacin.

Gwamnan ya ce, tunin gwamnatin jihar ta bayar da wasu aiyukan a wurare daban-daban domin kyautata harkokin kasuwanci, sufuri da bunkasar tattalin arziki, yana mai cewa dukkanin wadannan aiyukan da gwamnatinsa ke yi, yana yi ne domin cika alkawuran da ya dauka wa jama’an da suka zabe shi, ya kuma sha alwashin baiwa marar da kunya.

Ya kuma ce, ba kawai za su zura ido ba ne, gwamnatin za ta sanya ido sosai wajen tabbatar da cewar aiyukan da suka bayar an gudanar da su a kan lokaci, kana an kuma gudanar da aiyuka masu nagatar domin jama’an yanzu da na gobe masu tasowa su mora, kana ya kuma tabbatar da cewar aiki ne suke yi babu kama kafar yaro.

A cewar Gwamna Bala, wannan aikin na shimfida sabon tituna da ya bayar, zai kyautata rayuwar dumbin jama’an da suke rayuwa a wadannan yankunan da kuma tabbatar da ci gaban kananan hukumomin biyu, jihar Bauchi da kuma kasar Nijeriya baki daya.

Bala Muhammad ya kuma nunar da cewar aiyukan raya jihar da kyautata wa jama’an jihar yanzu ne ma gwamnatinsa suka faro, don haka ne ya nemi hadin kan jama’an jihar domin gwamnatinsa ta samu nasarar cimma kyawawan manufofin da ta zo musu da su.

Tun a farko da yake karin haske kan aikin da aka bayar da gudanarwar, babban sakataren dindindin a ma’aikatar aiyuka da sufuri na jihar Bauchi, Injiniya Stephen Abubakar ya shaida cewar muddin aka kai ga kammala wadannan aiyukan, za su kawo ci gaba ta fuskacin kyautata jin dadi da walwalar jama’a, samar da aiyukan yi da kuma sauwake wa jama’a dawainiyar sufuri da zirga-zirga musamman wajen kwaso amfanin gona.

Ya kuma fadada bayani da cewar an tsara aikin hanyar ne mai nisan kilomita 58.4km da zai kasance ke da fadin mita 10.3m, inda fadin layin mota zai kasance mita 7.3m da kuma dan sararin hanya (Shoulders) mai fadin mita 1.5m a kowace layi da titin zai ratsa.

Sakataren ya kuma ce, dukka a cikin kwangilar da aka bayar din, za kuma a gina manyan gadoji guda hudu (4) da kwalbati-kwalbati guda 45 hadi da wasu karin kwalbatoci kanana guda 70 da za samar da su, wanda ake fatan kammala dukkanin aiyyukan a cikin watanni 24.

Shi kuwa shugaban riko na karamar hukumar Tafawa Balewa wanda ke bayani a madadin wadanda za su ci gajiyar aikin, Barista Kefas Magaji, ya jinjina wa yunkurin gwamnan jihar da gwamnatinsa kan kawo wannan aikin a yankin nasu, a cewar shi, tabbas aikin zai taba rayuwar jama’a sosai wajen bunkasa harkokin sufuri musamman wajen kyautata zirga-zirgan amfanin gona, ya shaida cewar babu abun da za su ce wa gwamnan sai godiya da fatan Allah taimaki gwamnatinsa.

Ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga jama’a da su kara ninka kokarinsu wajen rungumar harnar noma, domin saukake wa gwamnati wasu abubuwan.

Ya roki jama’an da za a gudanar da aikin a yankunansu da cewar su yi kokarin bayar da hadin kai wa ma’aikatan da za su gudanar da aikin domin a samu nasarar cin gajiyar aikin yadda ya dace.

Manajan kamfanin TRIACTA Nigeria Limited ya ce, kamar yadda gwamnatin ta amince musu wajen basu wannan aiki, za su tabbatar da gudanar da shi a kan lokaci kuma mai nagarta wanda za a jima ana mora, ya bayar da tabbacin nasarar aikin ga jama’an yankina.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: