Connect with us

RA'AYINMU

Hadin Kai Da Kishin Kasa Ake Bukata A Halin Yanzu A Nijeriya

Published

on

Tun bayan sake dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999, Nijeriya ke fama da wasu abubuwa masu kama da cin-karon-juna, tare da ci-gaba da yin korafe-korafe daga wurin kananan kabilu wadanda ta karfin tsiya Sojoji suka murkushe su. Domin jan hankalin Shugabannin siyasa, wadanda suka samu nasarar karbar mulki daga wajen Sojiji, Kabilu daban-daban sun ta faman fadi-tashin yadda za a ba su damar cin gashin kansu a bangaren day a shafi arzikin kasa, sake sauya fasalin Gwamnati, samar da ‘Yan Sandan Jihohi da sauran makamantansu.

Har ila yau, sai aka yi rashin sa’a; Shugabannin siyasa su ma suka dauki irin wancan salon na Sojoji, na yin watsi da wadannan kananan kabilu tare da fifita manyansu. Ko shakka babu, wannan na nuni tare da tabbatar da cewa, sun dauki hanyar rura wutar rabe-raben kawuna tare da kawo barazana kan hadin kan ‘yan kasa.

Babu shakka, ire-iren wadannan sun haifar da rashin yarda a kan Shugabannin siyasa a wajen fusatattun ‘Yan Nijeriya, wadanda suka hada kansu wuri guda, suka kafa kungiya domin ganin abin da suke bukata ya samu ko ta halin kaka. Kazalika, asalin wadanda suka assasa wannan kungiya suke kuma kashe mata kudi, wasu ne wadanda aka taba damawa da su a Gwamnatin baya, suke kashe ko dai halastattun kudaden da suka samu, ko kuma na al’ummar Nijeriya da suka sata.

Haka zalika, kungiyar na da karfi, sannan sun yi mata kyakkyawan tsari da kuma shiri. Haka nan, mutane ne wadanda a lokacin da suka samu damar tafiyar da Gwamnati, mutane sun tsane su, sakamakon irin kama-karya da suka rika faman yi yadda ransu ke so. Babban abin da suka sanya gaba a halin yanzu shi ne, kalubalantar kudire-kudiren Gwamnati, ayyukan da ta sanya gaba da kuma sauran tsare-tsare da shirye-shiryenta, musamman idan ya kasance ba su a bangaren da ba sa so ne ko suke adawa da shi.

Kodayake, suna ikrarin cewa, suna yin fada da adawa ne domin talaka, ba don kansu ba, bayan kuwa duk abin da suke yi, suna yi ne domin gyara siyasarsu da kuma manufar da suka sanya gaba, da ya hada da ‘ya’yansu da kuma matansu kadai. A lokacin da suka samu dama a Gwamnatin baya, sheke a yarsu kawai suka rika yi, suna abin da ransu ke so. Don haka, yanzu suna yin amfani ne da wancan ilimi nasu, don kokarin ganin sun sake samun wata Gwamnatin, musamman a Tarayya; domin ci-gaba da lalata al’amuran wannan kasa.

Irin wannan dama da wadannan Shugabanni marasa kishin kasa ke nema, ita ce ke birge Matasa tare da ba su sha’awa, da sunan ana so a kwato wa talaka ‘yancinsa, a kuma kawo a gyara a cikin kasa, ko da kuwa abin da ake fada musu din karya ce da son zuciya tsantsa.   

Har wa yau, wannan ba karamin abin jajantawa ba ne da kuma ban tsoro a fadin wannan kasa. Mu a namu ganin, wadannan tsofaffin marasa kishin kasa, na son yin amfani da Matasa ne musamman marasa aikin yi, domin biyan bukatun kashin kansu. Musamman idan aka yi la’akari da yanayin matsi wanda yanayin tattalin arziki ya jefa mu a ciki, wannan zai ba su damar yin amfani da wadannan Matasa a arha ba tare da suna kashe makudan kudi ba.

Saboda haka, babban abin tsoro a nan shi ne, ba a taba samun rarrabuwar kawuna a tarihin Nijeriya kamar irin na wannan lokaci ba, wanda ke kawo barazana tare da sake rura wutar kabilanci da rarrabuwar kai, baya ga matsalar sha’anin tsaro da ya addabi wannan kasa.

Don haka, wannan Gidan Jarida, ko kadan baya goyon bayan wannan mummunan hali da wadannan Shugabanni marasa kishin kasa ke son sanya Nijeriya a ciki. Sannan muna jan hankali tare da baiwa wadannan Matasa shawara, wadanda ke son bin wadannan gurbatattun Shugabanni, da su yi karatun na nutsu, su yi watsi da ire-iren wadannan kiranye-kiranye wanda ka iya jefa su ga halaka ko wani mummunan hali. Muna sake kira ga ku Matasa a duk inda kuke cikin fadin wannan kasa, da ku nuna wadannan gubatattun Shugabanni cewa, yanzu fa tuni kan mage ya waye, babu wani wanda zai zo ya yi amfani da ku don biyan bukatar kansa.

Haka nan, ya kyautu Gwamnati mai ci a halin yanzu, ta dauki tsauraran matakai a kansu, domin tabbatar da gaskiya da zaman lafiya, sannan ta yi duk irin abin da ya kamata don tabbatar da hadin kan ‘yan kasa da kuma kawar da rabe-raben da ke tsakaninsu, sannan a karawa Jihohi karfi domin rage neman manyan mukamai a Gwamnatin Tarayya da kuma neman yawan kudaden shiga daga wurinta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!