Connect with us

LABARAI

Hukumar TCN Ta Dora Wa KEDCO Alhakin Rashin Wuta A Kano Da Jigawa Da Katsina

Published

on

Hukumar samarda wutar lantarki ta kasa.TCN ta dorawa kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO alhakin rashin wuta da ake fama dashi a jahohin Kano,Katsina,Jigawa da wasu sassa na Bauchi sakamakon kin karbar wutar da ta yi.

Wani babban jami’i a TCN Injiniya Kamal Bello ya shaidawa manema labarai cewa sakamakon kin karbar wutw da KEDCO sukayi tasa jama’arda ke karbar wuta karkashin KEDCO shiga mawuyacin hali alhali kuwa akwai wutarna  a hukumar ta TCN a jibge.

Yace tabbas a yan kwanakin baya sun umurci KEDCO su rufe wasu layukan bada wutar lantarki  guda Biyu  daga cikin 32 da suke dasu a Kano dalilin rashin biyan wuta da KEDCO ta gazayi ga hukumar ta TCN su kuma sai suka koma suna hana wutar ga al’umma.

Injiniya Kamal Bello yace yanzu sakamakon rashin karbar wutar da KEDCO take wutar lantarkin tayiwa runbum TCN bozo dole sai dai su rika tsiyayarda ita ta zuketa domin yin hakan shine zai zame musu kandagarki  domin karta jawo musu babbar asara da zatayi musu mummunar barna.

Su dai Kamfanin na KEDCO ko a baya sun koka da cewa suna bin dinbin bashin biliyoyin Nairoro a wajen jama’a wanda shine ke jawo musu tarnaki wajen rashin biyan wutarda suke karba dan rarrabashi ga jama’ar.

Sai dai jama’a da dama na zargin KEDCO musamman a Kano dayin dungushe wajen basu wutar lantarki takai ma a wasu unguwannan bai wuci su sami wuta na kwanaki hudu a cikin wata guda ba,amma sai kawai a kawo musu bil na biyan kudin wata.

Wani ya shauda mana cewa wani abin takaici shi ne sai kaga a karshen wata sun tsiri baku wuta na yan kwanaki suzo su karbi kudin wuta da an sake tura kwanaki a sabon wata shike nan bazasu sake kawowa,hatta masu amfani da mita suna kukan rashin basu wuta sannan kuma sai asa cajin kudin katin mitar ya rika ja da gudu wannan duk na daga matsaloli da ke sawa mutane basa bada cikakkiyar goyon baya ga kamfanin na KEDCO.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!