Connect with us

LABARAI

Kotun Sauraron Koken Zabe A Kaduna Ta Tabbatar Da Zaben Sanata Uba Sani

Published

on

Kotun dake sauraron koken zabe na Majalisar kasa dana Majalisar johohi dake zaman ta a jihar Kaduna a karkashin Alkali Mai Shari’a A.H Suleiman ta kori koken da dan takarar jamiyyar PDP Lawal Adamu Usman  daka ake yiwa lakabi da (Mr LA) ya shigar a gaban ta.

Lawal Adamu ya maka Sanata Uba Sani a gaban Kotun ne wanda a yanzu yake wakilatar mazabar Kaduna ta tsakiya a karkashin inuwar jamiyyar sat a APC mai mulki, inda yake kalubalantar zabar da aka yiwa Sanata Uba Sani.

Alkali Mai Shari’a A.H Suleiman a jiya Asabar ne ya yanke hukuncin bayan ya shafe awa biyu, inda Alkalin ya ce, wanda ya gabatar da korafin a gaban Kotun Lawal Adamu Usman ya gaza gabatar da kwararan hujjo, inda y ace, dukkan shedar day a gabatar ya gabatar dasu ne a bisa jita –jita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!