Connect with us

LABARAI

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari Za Su Yi Aiki Tare Da Sabon Shugaban Kasuwar

Published

on

Kungiyar  yan kasuwar Kantin kwari sun tabbatar da gamsuwa da goyon bayansu bisa nadin da Gwamnan Kano ya yi wa kasuwar na kawo musu sabon manajan daraktar hukumar Kasuwar. Shugaban Kungiyar kasuwar Alhaji Ahmad Sani Namado ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce akwai tsare-tsare  amma daidaikun mutane a kasuwar saboda suna ganin sun isa da karfin kudi ko kata isa da suke ganin kungiyar ba Gwamnati ba ce, kana da dama kace baka ciki kamar yanda wasu tsiraru suke duba da wannan sai abubuwa suzo na alkhairi amma saboda son zuciyar daidaiku sai su bijirewa tsarin ya cutar da al’umma.

Namado ya ce wata kila Gwamnati ta dubi irin wannan ta gani sai tayi shawarar ta kafa wata hukuma wanda in akade ga wani abu  yazo kasan cewa kai tsaye daga Gwamnati ne. Don idan ana maganar M.D. za’a bashi ma’aikata zai kawo abinda akeso Gwamnati nada ido a kasuwa a kan abinda za ta yi. Su a matsayinsu na shugabannin kungiyar kasuwar wannan hukuma an kara musu karfi ne sa za su yi aiki tare su ciyar da kasuwar gaba domin shi manajan daraktan da aka kawo idone na Gwamnati su kuma yan kasuwa in suka hadu akwai matsalolu da za su haska a kawo gyara don cigaba.

Ya bada misali da yanda kungiyar ta sanya masu shaguna su rika biyan N1000 a duk karshen wata. A baya ba kudi da ake karba na gudanar da tsafta da tsaro sama da shekara daya da watanni biyu basu karbi wani abu ba, amma a haka suka sayi motocin aikin kwashe shara guda shida da suke aiki kullum wanda tasa a  bana ma sakamakon kula da tsafta da magudanan ruwa ba’a sami ambaliyar ruwa da aka saba gani a kasuwar ba. Amma a haka wasu ke rufe ido suke kin goyawa kungiyar baya duk da ba sun akan son zuciya  bane  sai don cigaba. Don haka suna maraba da duk wanda za’a kawo  suyi aiki dashi  fatansu shima manajan daraktan ya zo sa burin cigaban kasuwa ta kawo hanyoyin magance matsalolin kasuwa a habaka tsaro da bunkasar tattalin arzikin yan kasuwa.

Alhaji Ahmad Nuhu Namado ya ce, duk wadanda suke korafin cewa ba’a dauko wani daga kasuwar an bashi matsayin manajan daraktan ba, to shi a ra’ayin kashin kansa  yanw murnw da kawo wani daga wajen kasuwar  saboda akwai abubuwa da ya kamata ayi ba-sani-ba-sabo,bai kamata a matsayinka na dan kasuwa an kawo cigaba amma son zuciya yasa a rika ganin cewa ba wanda ya isa.

Shugaban kungiyar kasuwar na kantin kwari Alhaji Ahmad Namado ya ce, akwai bukatar Gwamnati  tasa hankalinta akan abubuwa dake tafiya yazo a kantin kwari in ana bakatar kasuwa ta ci gaba akwai abubuwa da ya kamata ayi tsayin daka domin akwai mutane da basa biyayya haka kawai basa biyayya ga shugabancin kungiyar kasuwar  wanda in ba’ayi tsayin daka a kansu ba haka za su cigaba da yi ba tare da wani dalili ba koda waye zai zo shugabanci. Saboda suna ganin sune ya kamata ace duk wanda ya zo su zai bi. A harkar shugabanci in aka ce akwai wannan a shugabanci da wuya wannan cigaba ya dore.

Namado ya yi kira ga yan kasuwar katin kwari su bai wa manajan daraktan kasuwar ta kantin kwari hadin-kai da goyon baya su sani ba wata hanya da za’a hadu a magance matsalolinsu su ciyar da kasuwancinsu gaba in bata kungiya ba domin ita ce uwa da uba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: