Connect with us

ADABI

Sharhi Da Fashin Baki A Kan Wakokin Shata Na Sarkin Bai Na Katsina Alhaji San Stores (2)

Published

on

To daga nan sai ya kuma ce : ‘Shi alheri kada ka fasa Store Sani…/ A nan, makadin ya san cewa alheri yana da abin da za ya haifas na alheri. Abubuwan da ya saba gani Sani Store na yin a kyauta da alheri, ta kada ya fasa ko ya bari, ya ci gaba da yi. Ko ba komi watarana za ya ga sakamakon abin, kuma sakamako mai kyau. Sai kuma

Dodo ya kara da cewa: Kuma Allah Ka arziki, Shi Yai maka shi a Birni, Store Sani/ Nan kuma Shata na nufin Sani Store ya yi ta hakuri da mutane tunda Allah Ya yi masa arziki, to za ya yi ta fuskantar kalubalen rayuwa da huzunu daga mutane, na kusa da na nesa, watau da na gida ‘yan uwa da ma bare wadanda ba jinin sa ba. To daga nan sai Duna na Bilkin Sambo ya ci gaba da cewa: Ya Allah don Allah, Jalla taimaka wa Store namu. Duk inda ka ji a waka, Shata na rokon Allah cewa, Ya taimaki wane, to a iya zaman da ya ke yi da mutumin nan ya hango akwai, ko dai wata makarkashiya ko wata mugunta ko wani munafunci da wani ko wasu ke kulla ma wannan mutumin. Don haka Shata na rokon Allah Ya fidda mutumin nan daga makircin wannan mutum ko wadannan mutane. Kuma na tabbata Shata ba ya fadin magana ta tashi a banza, na tabbata da kalmomin da ya fadi a sama akwai alamun ya ga akwai wani abu a kasa. Da an duba za a ga akwai abin nan da ya ke fadi.

Wakar da ya yi masa ta biyu, amshin ta shi ne: Sarkin Bai Haji Sani Store/ Ya fara budewa da Dottijo mai abin arziki, Sarkin Bai Haji Sani Store/  Ma’ana: duk inda ka ji Shata ya ce ma mutum ‘dottijo’, to yana nufin mutum kamalalle, mai hakuri, wanda idan ya ce ma Shata ya bari, to za ya bari, idan kuma bai yi niyyar yin abu ba, idan ya ce masa ya yi, to sai ya yi, bisa ga ganin girman wannan mutum. Wannan shi ne ‘dottijo’ a wurin Shata. To a Katsina, Stores ya kan tilasta ma Shata ya yi abu, ko da bai yi niyyar yi ba, sabili da la’akari da shi ubangidan sa ne. Da kuma ya ambaci kalmar A dai gaida ku, a dai gaida mu….’ Yana nuna godiya ga Allah, cewa shi da yaran sa sun yi kokari, sun yi kokarin yi ma Stores kirari, shi kuma Stores, a gaida shi da kokarin rike Shata da yaran sa.

Shata ya bayyana cewa Na san Birnin Dikko da farko, karshe na san Birnin Dikko dalilin Alhaji Sani Stores/ Ka ga waccan magana ta farko ta fito, ta cewa zuwan Shata Katsina na farko ba ta dalilin Stores ba ne, watau cikin 1944 na nadin Sarki Usman Nagogo (1944-1981) da kuma 1947 na zuwa auren Wakilin Doka Kabir Usman, amma sai ya ce daga ‘karshe’, watau zuwn sa daga bisani, ta dalilin Sani Stores ya ke zuwa, kafin ya gane Katsinawan Dikko kenan.

Sai kuma ya ce wannan ya rike amanar talaka ya kuma rike amanar Sarki, kowanne, na yi masa murna, maraba da Alhaji Sani Store/ wannan kuma sha’anin aikin NA ne da Stores ya yi aiki ba a taba kama shi da laifin ya dauki kudin baitulmali ba. Ka ga a nan, an tsare amanar kasa da ta Sarki tunda a lokacin NA na a karkashin ikon Sarki. Shata kuma a ce : kai yara za ni Birni in kwana, Sarkin Bai Haji Sani Stores/ Yana yi ma mai saurare tuni cewa a wancan lokaci domin Stores ya kan tafi Katsina.  Ya kuma ce: Baba dottijo, mai abin arziki/ Abin arziki dais hi ne ‘hakuri’ don hakuri shi ke cim ma rabo, kuma duk wani arziki a Duniya, farkon sa hakuri ne. Kalmar ‘Baba’ kuma na nufin wanda ya isa a wurin Shatan. Ya kuma kara kaurara Kalmar, da ya nanata Ga ka dottijo dan dottijo….’ Yana son ya kara bayyana ma Duniya cewa lallai Sani Stores mai hakuri ne, kuma ya yi gadon hakuri wajen mahaifin sa.

Kuma zancen yaran Birni sun gode maka, manyan Birni na murna tasa, Sarkin Bai Haji Sani Stores/ to babu shakka Shata ya taba ganin almajirai da sauran mabukata sun yi dafifi a kofar gidan Sani Stores suna amsar sadaka da abinci. Da an bincika za a ga hakan, domin abin da ya ke nufi kenan. Wasu baitoci na gaba kuma mas zuwa yana cewa: Zan tafi in ishe Sani Store/ Yanzu ku ‘yan yara a mota na sauka, zan je in ishe Sani Store/ To nan, yana nufin Sani Store kan zama abokin shawara ga makadin, cewa idan wani abu ya shige masa a cikin duhu, to bari ya tafi ga ubangidan sa ya nemi shawara domin samun mafita.

Cikin 1976 kuma aka nada shi Turakin Katsina, nan ma makadin kan ziyarce shi domin tama shi murna har ma ya taya shi hira. Waka a wurin Shata ba abin wahala ba ce amma wani lokaci kan zo, wanda za ya bijiro da a yi ma mutum wakar. Amma a wannan sabuwar sarautar Shata bai yi masa sabuwar waka ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!