Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din “Burina”

Published

on

Suna: Burina.

Tsara Labari: Musa Namalan Bole.

Kamfani: NICE Entertainment Nig. Ltd.

Daukar Nauyi: NICE Entertainment Nig. Ltd.

Shiryawa: Musa Namalan Bole.

Bada Umarni: Ali Nuhu.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Nafisat Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Shu’aibu Lawal Kumurchi, Ladidi Fagge, Abbas Sadik, Musa Namalan Bole, Bala Anka Gwada, Asma’u Nass, Amina Minna, Sani Sanki Show, Maijidda Minna da sauransu.

Fim din “Burina” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata matashiya mai suna Surayya( Nafisat Abdullahi). Ita dai Surayya ma’aikaciyar tsaro ce wacca ta ke aikin Dan Sanda, kuma ta na da kwarewa sosai a wannan aikin nata. Hakan ne ya sa ma ta daura gabaran neman wani shahararren Dan ta’adda mai suna T. J(Shu’aibu Lawal Kumurchi) sakamakon shaharar da yi a wannan ta’adaccin nashi, Kuma ta samu nasarar kama shi Kuma ta mika shi zuwa gidan yari.

A daya bangren Kuma, Surayya ta kasnce ta na tsananin soyayyar wani jarumin fina-finai mai suna Anas (Ali Nuhu), sai dai ita tata soyayyar ta zo da wani sabon irin salo ne, domin ita bayyanawa ta ke duk duniya ba wanda ta tsana kamar Anas din. Domin kuwa har hira ta yi a gidan T.B tana bayyanawa duniya irin kiyayyar da ta ke masa. Duk da cewa mahaifiyarta da kanwarta Asma’u kullum su na mata fada a kan abun da ta ke yi wa Anas.

Ana haka ne wataran Anas da mahaifinsa(Rabi’u Rikadawa) da mahaifiyarsa(Ladidi Fagge) su na zaune kawai sai a ka hasko Surayya a T.B tana bayyana irin yadda ta tsani Anas. A lokacin ne mahaifinsa ya ke tambayar Anas a kan me ne ne ya ke a tsakaninsu har ta ke iya bayyana kiyayyarta haka a fili a gareshi? Shi ne ya ke fada masa cewa shi bai ma san ta ba,Kuma bai ma taba ganinta ba. To shi ne baban ya ce masa lallai ya neme ta ya ji me ya sa ta ke yi masa haka. Hakan kuwa a ka yi, Anas ya taka ya je har ofishinsu Surayya domin su tattauna, sai dai ta ce masa ba ta da lokacin yin magana da shi a ofis,idan ya na so su yi magana to ya same ta a wani wajen cin abinci da daddare.

Da daddaren Anas ya je ya same ta a wajen da su ka yi alkawarin haduwa, inda a nan ta ke fada masa cewa ita fa tsananin kaunar da ta ke masa ne ya sa ta zuwa da wannan salon na nuna kiyayyarsa, amma ita wlh ba wanda ta ke so duk duniya kamar shi. Anas ya na bude baki sai ya ce mata ba ya cikin mutanen da za ta iya rainawa hankali yadda ta ke so. Ya ce bayan ta gama bayyanawa duniya irin kiyayyar da ta ke masa, kuma sai yanzu ta dawo ta ce tana son shi, ya ce sam wannan ba zai yi wu ba, kuma ya ce da ya san abinda za ta fada masa kenan da bai bata lokacinsa ya zo gurunta ba. Kawai sai ya tashi ya yi tafiyarsa ya bar ta a nan.

Da Surayya ta ga wannan tsarin nata bai kai mata ba, sai ta sake sabon salo ta hanyar sanyawa Anas gawa a cikin motarsa, Kuma ta yi ta bin sa a baya da mota bayan an saka gawar domin ta ga ya zai yi da gawar. Anas bai san da gawa a motarsa ba har sai da su ka tsaya da abokinsa a wani kanti domin su sayi ruwa, bayan sun siyo ne kawai ya zo ya bude bayan motar domin a saka ruwan a ciki kawai sai ya ga gawa. Ai kuwa nan take sai ya yi sauri ya rufe motar. Bayan sun taho ne sai su ka yanke shawara da abokinsa a kan su je su jefar da wannan gawar. Ashe lokacin da su ka je za su jefar din Surayya ta na bayansu ta na kallon su kuma ta dauke su a hoto a lokacin amma su ba su sani ba.

Bayan an kwana biyu, sai Surayya ta je ta sami Anas a wajen daukar fim dinsu, shi ne ta nuna masa hotunan lokacin da su ke jefar da gawar. Sai Anas ya ke fada mata cewa wallahi ba shi ya kashe ta ba, sai ta ce masa ta ya ya za ta gane hakan, idan ya na da wani jawabi to ya same ta a ofis. Ai kuwa cikin rawar jiki Anas ya je ya same ta a ofis din, a nan ta ke fada masa cewa za ta rufa masa asiri amma da sharadin sai dai idan ya amince zai aure ta cikin sati biyu. Hakan kuwa a ka yi, domin kuwa Anas ya auri Surayya, bayan an yi auren ne ta ke fada masa duk abunda ta tsara domin burinta ya cika a kanshi, sannan ta nemi ya yafe mata, nan su ka ci-gaba da rayuwarsu cikin farin ciki da soyayyar juna.

ABUBUWAN YABAWA

1. Sunan fim din ya dace da labarin duba da yadda burin Surayya ya cika a kan Anas.

2. Labarin fim din bai karye ba tun daga farko har karshe.

3. Fim din ya samu aiki mai kyau.

4. Jaruman sun yi kokari wajen isar da sakon da fim din ya kunsa.

5. Sauti ya fita duk da dai ya na shakewa a wasu gurare a cikin fim din.

KURAKURAI

1. A matsayin Surayya na jami’ar tsaro ta ya ya za ta je ta na hira a gidan telebishin ta na cewa ta tsani wani dan fim, daman ana irin wannan hirar da ‘yan sanda a kafafen yada labarai?

2. An samu sabawar hotuna da kuma sautin magana.

3. Daukar fim din ba ta yi kyau ba musamman farkon fim din zuwa tsakiyarsa.

4. Neman soyayya da salon bayyana kiyayya bai cika kai wa ga nasara ba.

5. An jiyo muryar Anas ya na ta cewa salamu alaikum har sau uku a lokacin da Asma’u ta ke fadawa mamansu cewa an sace Surayya, Kuma alhalin babu Anas ma a cikin wannan fitowar, to me ya kawo muryarsa?

6. A farkon fim din an nuno wani ya kusa bige wani da mota amma bai buge shi ba, amma kuma a karshe sai a ka nuna irin wannan fitowar dai a ka nuna Anas ne ya buge shi. Fitowa iri daya, ba a buge shi a ta farko ba, an buge shi a ta biyu.

KARKAREWA

Fim din “Burina” fim ne da ya yi kokari wajen isar da sakon da a ke so ya isar ga masu kallo. Duk da nasarori da fim din ya samu, amma yana dauke da wasu kurakurai da bai kamata a ce an bari sun iso ga mai kallo a haka ba. Saboda kurakurai ne da za a iya magance su tun kafun a saki fim din ya fito. Yana da kyau daraktoci su ringa maida hankali wajen lura da duk wasu matsaloli da za su iya bai wa fim dinsu damuwa. Ya na da kyau su sani cewa duk nasarar da a ka samu a cikin fim to aikin darakta ne, haka idan a ka samu akasin hakan ma to darakta ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!