Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Chana Sun Jima Suna Durkusar Da ‘Yan Kasuwar Arewacin Nijeriya – Dubji

Published

on

An bayyana irin rikon sakainar kashin da Shugabanni da sauran Hukumomin Gwamnati, ke yi wa dokar harkokin kasuwanci ta shekarar 1972, zuwa shekarar 1976, inda dokar ta tsara yadda hurumin kowa zai kasance a harkar kasuwanci tsakanin ‘Yan Kasuwarmu da kuma bakin haure. Yin shakulatin bangaro da wannan doka ne, ya jefa dubban ‘Yan Kasuwa da ke sana’ar saye da sayarwa a Kasuwannin Arewacin Nijeriya, cikin wani mawuyacin hali.

Jawabin haka ya fito ne daga bakin Alhaji Muhammad Abdullahi Maidibji, guda cikin Dattawan kasuwar Kantin Kwari, a lokacin da yake amsa tambayoyi a kan halin da ‘Yan kasuwar ta Kantin Kwari suka tsinci kansu, sakamakon yadda ‘Yan China suka zama hayaki fidda na kogo.

Maidibji ya kara da cewa, ‘Yan Chana sun samu damar shigowa Nijeriya ne, a wancan

lokaci sakamakon rufe Masakun Kasar nan da aka yi. Farkon zuwansu, sun bi doka da

oda wajen tafiyar da harkokinsu, kuma dubban Jam’a sun amafana tare da yin farin ciki da zuwan wadannan ‘Yan Chana.

Haka zalika, ya ce yau dai kimanin shekaru 20 kenan, da Kamfanonin Atamfa na Kasar China suka shigo Kasuwanninmu na Arewacin wannan kasa, musamman a shahararriyar Kasuwar Atamfofi da Shadda ta Afirika, wadda aka fi sani da Kantin Kwari a Jihar Kano.

Babu shakka, wannan shigowa ta bakin namu na da amfani idan aka yi la’akari da yadda dokar shekara ta 1972  zuwa 1976, wacce ta tantance hurumin kowa ta fuskar Kasuwanci tsakanin ‘Yan Kasuwar Gida Nijeriya da na Kasashen Waje.

Amma abin takaici,  rashin amfani da  wannan doka  da sakacin Jami’an kula da harkokin Kasuwanci na Jihohi da na Tarayya, shi yasa Kamfanonin Atamfa na Chana  a halin yanzu suka dagula harkokin kasuwanci  a Kasuwanninmu  da ke mu’amala da harkokin Atamfa da sauran yadiddika, al’amarin ya fi illata ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari kwarai da gaske.

Dattijon Kasuwar ta Kwari, ya bayyana yadda da farko ‘Yan Chana suka shigo Kasuwar, inda suke cinikin Kwantena-kwantena kawai a lokaci guda kuma sai suka koma suna karbar oda daga hannun ‘Yan Kasuwa, ‘Yan Kasa. Amma abin takaici yanzu, ‘Yan Chana sun shiga harkar sayar da Atamfa turmi-turmi a cikin kasuwanninmu, wanda hakan karya waccan dokar cinikin ce, wadda hakan yasa aka mayar da ‘Yan Kasuwarmu dillalai, sannan kuma hakan ba karamar

illa ce ga ci-gaban harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasarmu ba.

Akarshe, Maidibji ya yi kira ga Hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci na Jihohi da na Tarayyar Nijeriya, su farka domin yi wa tufkar hanci kafin  durkusar da ‘Yan kasuwarmu baki daya, Gwamnati ta yi kokarin shigowa cikin lamarin domin tabbatar da bin doka da oda ga wadancan bakin haure, wanda idan ka shiga kasashensu ba ka isa ka kamanta irin haka ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: