Connect with us

LABARAI

An Yi Bikin Nadin Sarautar Sarkin Fulanin Karamar Hukumar Lokoja

Published

on

Al’ummar Fulani makiyaya daga sassa daban-daban na najeriya a ranar Juma’a da ta gabata sun hallara a fadar Sarkin Lokoja don shaida bikin nadin sabon sarautar Sarkin Fulani (Ardo) na yankin karamar hukumar Lokoja, Alhaji Muhammadu Abubakar Duni.

Bikin, wanda ya samu halarcin kungiyoyin Fulani daban-daban da masu rike da rawanin sarki da yan siyasa da kuma sauran al’ummar karamar hukumar Lokoja, ya kayatar matuka gaya.

Da ya ke jawabi a wajen bikin, Mai Martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi na III, wanda Wazirin Lokoja, Alhaji Abdulrahman Babakurun ya wakilta, kira ya yi ga Sabon Ardon na Fulani da ya gudanar da nauyin da al’ummarsa su ka dora ma sa ba tare da nuna son zuciya ba.

Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi har ila yau ya bukaci sabon sarkin na Fulani da ya rika hada kai da sauran Fulani wajen yanke shawara don a gudu tare a kuma tsira tare don ci gaban al’ummar na Fulani.

Mai Martaba Sarkin na Lokoja kazalika ya yi kira ga Alhaji Muhammadu Abubakar Duni ya yi amfani da matsayinsa na shugaba wajen hada kawunan al’ummar Fulani makiyaya domin samun zaman lafiya da ingatuwar tattalin arziki da kuma zamantakewar al’ummar Fulani da ke karamar hukumar Lokoja da kuma sauran kananan hukumomin da ke jihar Kogi.

Alhaji Kabir Maikarfi wanda har ila ya yi waiwaye baya ga irin rawar da Marigayi Ardon Fulani Alhaji Abubakar Duni ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummar Fulani, ya kuma kira ga Sabon Ardon na Fulani da ya yi koyi da mahaifinsa.

Sarkin na Lokoja har ila yau ya tunatar da sabon sarkin na Fulani da cewa ’yan uwansa Fulani ne su ka amince da shi kuma su ka gabatar da shi a matsayin Ardonsu kafin ya nada shi. A kan haka ne ya nanata kira ga Sabon Ardon na Fulani da ya yi adalci tare da bai wa kowa hakkinsa ba tare da nuna son kai ko son zuciya ba, inda har kuma ya bukace shi da ya yi biyayya ga masarautar ta Lokoja ganin cewa a yanzu ya zama da ya daga cikin masu rawanin sarki.

Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi na III ya kuma yabawa al’ummar Fulani a karamar hukumar Lokoja a bisa zaman lafiya tsakaninsu da sauran al’ummar karamar hukumar, inda ya yi fatan hakan zai dore.

Da ya ke godewa Sarkin Lokoja game da nadin, Sabon Ardon na Fulani a karamar hukumar Lokoja, Alhaji Muhammadu Abubakar Duni Yayi alkawarin sauke nayin da al’ummarsa na Fulani suka dora masa. Alhaji Muhammadu Abubakar Duni ya kuma yi alkawarin yin koyi da halayen marigayi mahaifinsa wanda ya gudanar da jagora na a lokacin yana raye.  Alhaji Muhammadu Abubakar Duni ya kuma godewa al’ummar Fulani makiyaya a bisa zabarsa a matsayin sabon Sarkinsu, sannan ya tabbatar musu da cewa zaiyi adalci ga kowa. Ya kuma yi kira ga yan’uwansa Fulani makiyaya dasu bashi cikakken hadin kai domin bashi daman gudanar da nauyin da suka dora masa cikin sauki,kana ya godewa dukkan wadanda suka halarci bikin.

Shi ma a nasa jawabin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi wanda ya samu wakilcin a sakataren kungiyar Fulani makiyaya ta kasa (MACBAN) reshen jihar Kogi kuma mai baiwa gwamnan sha’awa ta musamman akan sha’anin Fulani makiyaya, Alhaji Suleiman Muhammed ya taya Sabon Ardon na Fulani murna,inda ya bukace shi da yayi amfani da daman daya samu wajen hada kawunan al’ummar Fulani a karamar hukumar ta Lokoja da kuma sauran al’ummar Fulani dake sauran kananan hukumomin jihar a matsayinsa na Ardon Ardodi a jihar Kogi.

Gwamna Bello har ila yau ya yiwa al’ummar Fulani dake fadin jihar samun kariya, sannan ya bukace su dasu zauna lafiya da junansu da kuma sauran al’umma masu masaukinsu a jihar. Kazalika gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Fulanin dasu kai rehotun duk wanda ke neman tada zaune tsaye ga hukuma domin daukar matakin gaggawa.

Daya daga cikin dattawan al’ummar Fulanin a jihar Kogi, Alhaji Dauda wanda ya yi jawabi a madadin sauran al, ummar Fulani ya sha alwashin yin biyayya ga sabon Ardon, Alhaji Muhammadu Abubakar Duni, wanda a cewarsa, Allah ne Ya zabe shi kuma Ya nada shi, inda ya ce za su yi ma sa biyayya duk da cewa ya na matashi.

Wakilan kungiyoyin Fulanin daban-daban da ke Nijeriya duk sun turo da wakilansu wajen bikin nadin, inda su ka gabatar da sakon fatan alheri ga sabon Ardon na Fulani a karamar hukumar Lokoja.

Bayan bikin Ardon ne kuma su ka kwana su na ajo da kade-kade da raye-raye irin na Fulani da kuma shadi, wanda matasan Fulanin su ka gudanar a filin makarantar firamare da ke Felele a Lokoja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!