Connect with us

LABARAI

An Yiwa Mata 681 Fyade A Jihohin Adamawa, Borno, Da Yobe – Cibiya

Published

on

Akalla an yi jima’i da mata 681 ba bisa ka’ida ba, a cewar wata cibiya mai mai tara bayanai kan cin zarafi ta fuskar jima’i, wato Sedual Assault Referral Centres (SARCs), bisa bayanan da ta tattara a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Cibiyar, wacce ke daukan matakan jinya da shari’a wadanda abin ya shafa kyauta, kungiyar hadin kan kasashen EU ta ke daukan nauyin gudanar da ayyukanta, ta bayyana haka ne ranar Laraba a wani taron tattara bayanan kwamitocinta a Abuja.

Da ta ke bada bayanai yi wa mata jima’i bada izini ba a jihar Adamawa, shugabar cibiyar a jihar, Dakta Usha Sadena, ta ce cibiyar da a ka fi sani da Hope Centre, ta fara aikinta a shekarar 2017, zuwa watan Yonin 2018, ta tattara rahoto 155.

Ta cigaba da cewa, “kashi 95 bisa dari na mutanen da lamarin ke shafa kanana ne, ta ce 18 daga cikinsu maza ne, sauran kuma duk mata, cikin rahoto 155, 27 ne kawai yanzu batunsu ke gaban kotu,” in ji Usha.

Ta yaba wa gwamnatin jihar da goyon bayan da ta ke bai wa cibiyar, musamman game da samar da mashunan tantance kwayar halitta DNA biyu, ta kuma yaba da samar motar daukan marasa lafiya (Ambulance), ga cibiyar da gwamnatin tarayya ta hanun PCNI ta yi.

Da shi ma ya ke jawabi, shugaban cibiyar a jihar Borno Kimba Goni, ya ce cibiyar da a ka fi sani da Nelewa Centre a jihar, ta fara ayyukanta a Fabrerun 2018, cikin wannan lokacin ta tattara rahoto 197, mafiya yawa suna gaban kotu, shida daga ciki sun amince da laifin da suka aikata.

Mista Kimba Goni, ya yaba da samun taimakon motar daukar marasa lafiya da gwamnatin tarayya ta yiwa cibiyar ta hanun kwamtin PCNI, yanzu kuma hukumar farfado da yankin arewa maso gabas (NEDC).

Da itama ke jawabi shugabar cibiyar a jihar Yobe Zainab Muhammad, wacce Musa Muhammad ya wakilta, ta ce an kafa cibiyar a shekarar 2016 a jihar, yanzu haka ta tattara rahoton yin jima’i bada izini ba 329, 309, mata 20 kuma daga ciki mazaje.

Ya ci gaba da cewa mafiya-yawan lamarin na gaban alkali, ya ce 46 daga ciki sun amince da laifinsu, haka kuma ya yaba da samun motar daukan marasa lafiya daga gwamnatin tarayya ta hanun PCNI.

Da shima ke jawabi a taron shugaban hukumar farfado da yankin arewa maso gabas North East Debelopment Commission (NEDC), Mohammad Alkali, wanda Musa Zarami ya wakilta ya ce hanyoyin da cibiyar ke bi wajan tantanci irin wadannan batutuwa a yankin da ayyukan ‘yan bindiga ya shafa abun a yaba ne, ya kuma basu tabbacin goyon baya.

Haka shima da yake jawabi shugaban cibiyar MCN, Farfesa Mohammed Tabiu, da Mista Ukoha Ukiwo, sun bayyana cewa taron na kwana biyu ya haifar da da mai ido, sukace kalubalen dake gaban cibiyar itace lalubo hanyoyin shawokan matsalar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!