Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Hanyar Minna Zuwa Bida Ta Zama Barazana Ga Rayuwar Matafiya

Published

on

Sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kimanin sati daya da ya gabata, hanyar Minna zuwa Bida ta lalace da ya zamarwa matafiya barazana.

Tun da farko kafin faruwar lamarin ta dauki lokaci tana sha faci-faci daga jama’a mazauna yankin da kuma wani lokaci hukumar kula da gyaran hanya ta jihar Neja kan yi kwaskwarimar da bayan ‘yan kwanaki biyu ta sake lalacewa, ko a shekarar bara saboda rashin kulawar gwamnati hanyar ta taba samun matsala saboda karyewar gada wanda sai bayan jama’a sun nuna bacin ransu saboda rashin kulawar da gwamnati tai wa hanya aka yi kokarin gyaran gadar, amma duk da hakan babbar hanyar wadda mallakin gwamnatin tarayya ne da ya tashi daga Minna zuwa Bida. ya bulle zuwa Mokwa da ke kan iyaka da jihar Kwara ta cigaba da nuna alamar gaji yawa amma duk da hakan ba wani kulawar da ta samu daga bangaren gwamnati.

Zuwa yanzu dai bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya yi sanadiyar salwantar da makuddan dukiyoyin jama’a, hanyar ta yi ragargajewar da ba yadda za a yi a cikin mintuna arba’in da biyar ka iya kaiwa Bida daga Minna sai ka dauki kusan awanni uku saboda cinkoson manyan motocin daukar kaya da ke fitowa daga jihar Legos dan saduwa da wasu jahohin kasar nan.

Jama’a da dama sun nuna fashin su akan sakacin gwamnatin jiha na rashin daukar matakin da ya dace tun kafin faruwar lamarin.

Da ya ke amsa tambayiyon manema labarai bayan ziyarci wajen. Babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da cigaban kasa, Alhaji Abubakar Sadik Balarabe ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta yi azama wajen duba hanyoyin da ta ke da ikon su a jihar nan.

Ya ce, gwamnatin jiha na kashe makuddan kudade, don kulawa da hanyoyin gwamnatin tarayya, akwai bukatar ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta dubi halin da hanyoyin jihar nan ke ciki.

Ya cigaba da cewar hanyoyin da ke bukatar kulawar gaggawa sun hada da hanyar Minna zuwa Suleja, Lambata, Lapai zuwa Agaie da Minna zuwa Bida, sai Mokwa zuwa Bokane, Tegina, da Tegina zuwa Kagara, Pandogari. Yace hanyoyin kan samu matsala ne a lokacin da ruwan sama ya sauka saboda zurga-zurgan manyan motocin dakon kaya da ke daukar kaya fiye da kima.

Manyan motocin dakon kaya su ne umulhaba’isin lalacewar hanyoyin mu, ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya da samar da wani shirin da zai tseratar da hanyoyin kasar nan daga lalacewa duba da illar da hanyoyin ke fuskanta a yanzu kafin abubuwa su yi tsananin da zai iya durkusar da komai.

Ya ce, motar da dakon kayan a za ta dauki tan 30 na kaya sai ka ga an dora mata tan 40 kuma a wannan hanyar za ta bi.

Kusan a kowani shekara sai an samu lalacewar hanyar nan a kallan wajaje takwas dan haka ya kamata gwamnatin tarayya ta umurci ‘yan kwangilar da aka yi yarjejeniyar aikin kilomita 86 daga Minna zuwa Bida na tagwayen hanya da su fara aikinsu.

Daga cikin matafyan da wakilin mu ya zanta da su, sun jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta mai da hankali wajen gyaran hanyar nan tun kafin abubuwa su tsaya, domin yanzu dole idan kana neman sauki sai dai ka bi ta Wushishi zuwa Bida ko kuma ta Lambata zuwa Lapai, Agaie kafin ka samu kaiwa Mokwa in kana son zuwa kudancin kasar nan ne.

Tun a shekarar bara dai gwamnatin jihar Neja ta bayyana a kasafin kudinta cewar Bankin Ja’iz zai aikin tagwayen hanyar daga Minna zuwa Bida wanda rashin daidaito da gwamnatin tarayya yasa har yanzu shiru.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: