Connect with us

LABARAI

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Karyata Batun Kona Mata Ofishi A Inugu

Published

on

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Inugu ta karyata rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kona ofishin ‘yan sanda, inda suka ce; babu wani ofishin ‘yan sanda da aka kona a fadin jihar. Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Ebere Amaraizu, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai a garin Inugu a ranar Lahadi.

Har wala yau, Amaraizu ya kara da cewa; wadansu bata gari ne suka je Ofishin ‘yan sanda dake Ikirike a karamar hukumar Inugu ta Kudu inda suka yi kamar sun kawo korafi ne, amma a karshe suka kaddamar da hari a ofishin da misalin karfe 8 na safe.

Ya tabbatar da cewa; babu dan sandan da ya rasa ransa a harin, amma an raunata wadansu ‘yan sandan, inda a halin yanzu ake duba lafiyarsu. Ya kara da cewa; bata garin ba su samu wata nasara ba a harin sakamakon gudummawar gaggawa da Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sulaiman Balaraba ya kawo ofishin. Sannan ya ci gaba da cewa; Kwamishinan tuni ya ba da umurnin fara binciken wannan aika-aika domin cafko wadanda suka aikata hakan.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: