Connect with us

Uncategorized

Karuwar Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Annoba Ce

Published

on

A kwanan baya ne wata kungiyar kare raji da ke yaki da cin hanci da rashawa da a turance a ke kira da SERAP ta gabatar da takardar koke a gaban Kotun Duniya da ke bin diddigin aikata manyan laifuka mai suna ICC a kan yawan karuwar yawan adadin yara da ke barin makarantu ba tare da kamallawa ba a daukacin fadin Najeriya.

A bisa alkaluman da a ka samar sun nuna cewa, yawan adadin yara da ke barin makarantu sun karu daga miliyan10. 5 a shekarar 2015 zuwa miliyan 13. 2 a shekarar 2018. Matsayin na kungiyar ta SERAP shi ne, gazawar shugabannin kasar wajen magance lamarin a daukacin fadin Nijeriya, inda hakan ne ya ke janyo cin zarafin yaran, kuma ya ke nuna cewa, hakan cin zarafin ’yan adam ne. Kungiyar dai ta mayar da hankali a kan dokar ’yancin yara kanana ta shekarar 2003 ne, wacce ta bai wa yara damar samun ilimin boko mai inganci.

Bugu da kari, wannan jaridar ita ma ta nuna nata jin zafin a kan lamarin, musamman ganin cewar duk dan Nijeriya mai kishi dole shi ma ya damu da yadda yaran su ke barin makaratanta ba tare sun kammala ba. Sai dai, lamarin ba wai a kasar ce kawai ya zamo ruwan dare ba, musamman ganin cewa, lamari ne da ya addabi daukacin fadin duniya.

Ala lmisali, kimanin yara miliyan 263 da ke a daukacin fadin duniya, ba sa halartar makaranta. Har ila yau, idan a bisa fashin bakin adadin da a ka yi, ya nuna cewa, yara miliyan 64 ’yan makatrantar firamare da shekarunsu su ka fara daga shida zuwa 11, inda kuma miliyan 61 da su ka kai munzalin balaga, kasa da ’yan makarantar da shekarunsu su ka kai daga 12 zuwa 14, ba sa zuwa makaranta, haka kuma wasu matasa miliyan 138 da su ke a makarantar sakadare da shekarunsu su ka kai daga 15 zuwa 17 su ma ba sa zuwa.

A wani rahoto da a ka fitar na duniya a kwanan baya ya nuna cewa, a Nijeriya yaran da su ka daina zuwa makaranta sun kai kashi biyu bisa uku kuma dukkansu sun fito ne daga gidajen talakawa, inda hakan ya nuna cewa, sun kai kimanin kashi 90 bisa 100. Sai dai, wannan adadin ya fi kusan hakan, domin ya kamata a sani cewa, ya kamata a sani kashi 69 bisa dari na yaran da su ka fice daga makaranta sun fi yawa a Arewacin Nijeriya, inda hakan ya ke sanya a cikin sauki a ke sanya su a cikin kungiyoyin aikata ta’addanci a wasu yankunan da ke cikin kasar.

Tabbas wannan lamarin kamar wani bpm ne da ya ke shirin tarwatsewa. A cikin shekaru 20 da su ka gabata da zuwa yanzu lamarin aikata ta’addanci iri-iri kamar na yin garkuwa da mutane, don karbar kudin fansa a kasar, sai kara zamowa ruwan dare ya ke yi da kuma kari da rashin daukar matasa ayyukan yi. Shin mene ne makomar Nijeriya idan har lamarin ya cigaba da aukuwa?

Amma mu na ankare da irin kokarin da matakan gwamnatoci daban-daban su ke yi wajen magance matsalar, musannam ta magance matsalar almajiri, inda wasu gwamnatocin da su ka gabata a baya kamar tsohuwar gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma na wannan gwamnatin mai ci ta fito da shirye-shirye na ciyar da ’yan makaranta abinci yadda za a kara bai wa iyayen yara kwarin gwiwa, don su rika sanya ’ya’yansu a makarantar firamre har da kuma wasu shirye-shiryen da matakan gwamnati a kananan hukumomi su ka kirkiro, don bai wa iyayen yara kwarin gwaiwa su sanya ’ya’yansu a makatranta.

Sai dai, a namu ra’ayin wannan kamar wata susa ce kawai, domin akwai abubuwan da su ka fi dacewa a mayar da hankali a kansu. A yau a Nijeriya abin ba a boye ya ke ba ganin cewa yara, musamman da su ke a cikin surkukin kauyuka da kuma yara masu fama da larurori iri-iri duk su na zaune a sansanin ’yan gudun hijira kuma a na fama da rashin isasassun kwararrun malamai da kuma makarantu.

Akwai kuma maganar tunanin da wasu su ke yi a kan alfanun ciyar da yaran ’yan makaranta da nuna jahilci a kan cewar da a ke yi a na bayar da ilimin zamani kyauta a makarantun gwamnati da kuma yadda ’yan kungiyar Boko Haram su ke ganin ilimin na zamani wani bin sahun shaidan ne kawai, inda hakan ya sanya su ka haramta ililimin na boko bayan alhali ilimin na boko tuni yankin Kudu maso Yamma su ka yiwa Arewacin Nijeya fintinkau.

Halayyar gwamnatocin Nijeriya, musamman a fannin zuba kudade a sashen ilimi, abin taiaci ne kawai. Daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2018 daga cikin adadin da a ka kebe wa fannin ilimin zamani bai wuce jimlar Naira tiriliyan ba. Duk da mahimmacin da ilimin na zamani ya ke da shi ya na samun dan somin tabi ne na Naira tiriliyan 3.90 kacal, wanda bai wuce kashi 7.07 bisa dari ba.

Duk a cikin wannan lokacin, fannin tsaro ya samu Naira tiriliyan 6.1 ko kuma kashi 10.51 bisa dari. Haka, a shekarar 2016, aikin hadaka na Gwamnatin Tarayya da jihohi 33 kasafin kudinsu a fannin ilimin zamani ya kai kashi 8.44 bisa 100 na jimlar kasafin kudadensu na wannan shekarar.

Masana a fannin sun yi jayayya cewar, shirin bayar da ilimi na bai-daya, an samu gazawa a Nijeriya, musamman ilimin makarantar Firamare a matakin Gwamnatin Tarayya, jihohi da kuma a kananan hukumomi.

Bugu da kari, a mafi yawancin jihohi ba a samar da kyakyawan yanayin da ya dace ba, musamman ganin cewa, gine-ginen makarantun duk sun lalace kuma ba a wadata makarantun da kayan aiki.

A bisa ra’ayin wannan jaridar, idan har ba a wadata al’umma da ilimin zamani ba, to fa akwai matsala babba. Akwai bukatar Nijeriya, ta yi gasa kafada da kafada a karnin tattalin arziki na 21, wanda ba wai lallai a fannin fasaha ba, a’a, har da fannin ilimi da adana bayanai.

A saboda wadannan hujjojin ne, mu ke yin kira ga matakan gwamnati da su bai wa ilimin zamani mahimmancin da ya dace ta hanyar zuba jari a fannin mai yawa. Ya kuma kamata a samar da kayan aiki yadda za a samar da al’umma ta gari. Daukacin matakan gwamnati da kuma kungiyoyi, ya zama wajibi su kara kaimi wajen yin gangami da wayar da kai, musamman a karkara ta yadda hakan zai sanya iyaye su bayar da hadin kai wajen sanya ’ya’yansu a makaranta don samun ilimin gwamnati kyauta.

Har‘ila’yau, ma’aikatu, sassa da kuma hukumomi su samar da dabaru wajen wayar da kan shugabbanni a kan ilimin zamani. Akwai kuma bukatar a shawo kan matsalar kai harin ta’addanci a Arewacin Nijeriya, idan a ka yi la’akari da yadda yawan yara da ke ficewa daga makaranta ya ke kara zamo wa ruwan dare a yankin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: