Connect with us

KAUCIN KABA SHA NEMA

Mallakar Miji (2)

Published

on

Maza Biyu, Halayya Daya:

Akwai maza iri biyu: Daya zai bayyana a fili, yayin da mace ta yi yunkurin sauya shi, cewa ba ta isa ba. Kuma ya ki sauyawa zuwa yanda take so din. Daya kuma zai yarda ya sauya zuwa yadda take so din cikin lumana. Amma kuma bayan wani dan lokaci da kansa zai koma yadda yake a baya. Maza dayan biyu ne; ko dai su bijire wa sauyin da mace take so ta yi musu kai tsaye, ko kuma su bujire a fakaice.

Idan har namiji bai gamsu har cikin ransa cewa lallai matarsa tana son sa a yadda yake ba, to ba zai taba iya zama abin da take so ya zama ba, ko da kuwa ya yi niyyar hakan. Domin idan ma ya fara tafiya a bisa turbar da take so, bai san lokacin da zai kuskure ya dawo kan ainishin dabi’arsa ba. A dabi’a irin ta namiji yana iya sauyawa daga ainishin tsarinsa zuwa yadda abokin zamansa yake so ne kawai, yayin da ya gamsu cewa an karbe shi a yadda yake, kuma ana son sa. Amma koma-bayan haka, duk wani yunkuri nasa ba ya samun cikakken hadin-kai daga can tushen dabi’arsa.    

Idan mace ba ta san wannan ba, sai ta yi ta faman bata lokacinta. Tsakanin kwalliya da suddabaru da girke-girke da shan magunguna, amma ta rasa gane ainishin inda mijinta ya dosa. Mata da yawa suna tsammanin maza suna da tsabar girman-kai ne ko kuma sun raina su. Shi ya sa ba sa daukar  shawarwari, ko karbar gyara idan ya zo daga gare su. Amma hakikanin lamarin shi ne, ba sa biyowa ta hanyar da idan suka kawo din mazan za u karba.

Namiji ba ya iya sauyawa daga ainishin dabi’arsa, sai lokacin da ya tsinci kansa a wani yanayi da ya gamsar da shi cewa, ana son sa. Kuma an yarda shi ma mutum ne mai daraja, mai hangen nesa, da azancin tafiyar da rayuwa daidai gwargwado. Ji a ransa cewa ana kallo ko daukansa a matsayin cikakken mutum, shi ne abin da yake tausasar dabi’arsa. Ya yi laushi, irin laushin da duka ba zai sa shi ya yi ba, balle yawan surutu da korefe-korafe.

Yayin da kake hira da mata masu cika baki. Daya daga cikin furucinsu shi ne: “Ni namiji a tafin hannuna nake ganin sa wallahi.” A bisa guntun nazarina, mafi yawan matan da suke irin wannan furucin sune kuma suka fi kowa shan wahalar mu’amula da maza. Domin wannan izzar da tunanin ba sa iya barin su su kwantar da kai yadda za su iya samun kan mazan. A wurin mata masu wayo da iya kwantar da kai, namiji tamkar rakumin da aka sanya wa akala ne, aka kuma danka musu akalar a hannu.

Maza Ba Sa Karbar Yunkurin Sauyi:

Kamar yadda maza suke ganin baiken mace yayin da ta dage tana ta fada ko korafi a kan wani abu, tare da cewa ga hanya magance shi nan cikin sauki. Haka nan kuma matan suke ganin baiken maza, yayin da suke ganin  ga hanyoyin rayuwa da a ganinsu su ne mafiya dacewa, amma mazan suke ganin laifi ne, a nuna musu hanyoyin.

Mata sukan sha mmaki da haushin, wai ya ya ma za a yi dora mutum  kan hanyar da za ta taiamake shi ya zama laifi! Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, maza suna kallon duniya ne da ido irin na duniyarsu ta maza. Tsarinsu shi ne: “Kar a sauya abu, sai ya gama watsewa.” Don haka, yayin da namiji ya ga mace ta dage a kan lallai sai ta sauya shi daga yadda yake, sai kawai ya dauka cewa ya tashi daga aiki. Don haka a irin wannan lokacin ba a bin da za a yi masa ya yarda cewa ana son sa. Kuma duk yadda zai yi ya nuna taurin kai, da tabbatar da cewa ba zai canzu ba, to sai ya yi.

Maza so suke a karbe su a yadda suke kawai. Karbar namiji a yadda yake da nuna masa yarda ba abu ne mai sauki ba. Amma tabbas idan har ana so a zauna lafiya da shi to dole ne a dauke kai daga tunanin sauya shi, rankatakaf. Kodayake, a wurin mace ba abu ne mai sauki a ce ta dauke kai daga tunanin ko yunkurin sauya mijinta ba. Dole ta ce da kai, “To ya ya kake so in yi?” Kina da gaskiya.

Ya Ya Mace Take Nuna Wa Namiji So, Ba Tare Da Ya Yi Zargin  Sauya Shi Take Son Yi Ba?

Daga muhimman matakan da suka kamata mace ta dauka wurin tabbatar wa namiji cewa ita fa ta karbe shi, ta yarda da shi, kuma tana son sa, sam ba yunkurin sauya shi take yi ba, akwai wadannan:

1. Kar ki rika yawan yi masa tambayoyi a lokacin da kika fuskanci yana cikin bacin rai.

2. Ki nuna masa kin damu da yanayin damuwa da ya samu kansa a ciki, amma kar ki nace sai kun tattauna kan abin da ya dame shi. Sai dai in shi da kansa ya nemi hakan.

3. Ki nuna masa yarda. Ki tattauna abin da ya dame ki game da shi, amma kar ki bari ya fahimci so kika ya sauya daga yadda yake.

4. Kar ki manta, ba bukatar ki yawaita ba shi shawara. Domin zai yi tunanin ba ki yarda da kaifin tunani ko hangensa ba ne.

5. Ki nuna masa ba sai ya zama kwararre ko gwani  sannan zai cancanci ki so shi ba.

6. Ki rika tunanin yi wa kanki wani abu da zai faranta miki rai da kanki. Ba wai dole dukkan farin cikinki sai ya zama daga gare shi ba.

7. Kar ki manta, namiji yana tuburewa ya ki karbar canji ne saboda yana zargin ba a son sa.

8. Kar ki manta, yin sadaukarwa don faranta masa, shi ne abin da yake yin tasiri a ransa, har ya kai shi ga sauyawa zuwa yadda kike so.

9. Za ki iya bayyana abubuwan da ba kya so a tare da shi, ba tare da nuna so kike ya sauya ba. Namiji yana iya sauwaya zuwa abin da kike so ne a kokarin yi miki sakayyar so da kyautatawar da kike yi masa.

10. Yayin da kike sanar da shi abubuwan da suke damunki game da shi, kar ki manta, ki yi da sigar da zai fahimci ba wai so kike ki nuna masa yadda ya kamata ya rika tafiyar da rayuwarsa ba. kawai dai kina so ya rika la’akari da taki maslahar ne.

11. Kar ki manta, idan kika zama ke za ki fadi yadda zai yi wani abu, zai ji tamkar ke kike juya shi.

Yayin da duk mace ta nakalci halayyar mijinta: Yadda ya kamata ta nuna masa yarda, cewa ta yarda da kwarewa ko gwanintarsa wurin gudanar da lammuransa. Da yadda za ta nuna masa cewa lallai ta karbe shi, a yadda yake, ba ta bukatar koya masa yadda zai yi rayuwa. A irin wannnan lokacin ne shi kuma zai ji tabbas tana son sa. To daga nan kuma canji zai fara samuwa, ba tare da ta nema ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: