Connect with us

RAHOTANNI

Mun Fara Jin Kunyar Jonathan – Ango Abdullahi

Published

on

Daya daga cikin manyan dattawan Najeriya, dan gwagwarmaya kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana cewa, a matsayinsu na wasu daga cikin wadanda su ka yiwa gwamnatin tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan na jam’iyyar PDP, taron dangi su ka kayar da ita a zaben 2015, inda shugaba mai ci, Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, ya kayar da Goodluck Jonathan din.

Farfesa Abdullahi ya bayyana hakan ne a tattaunawar musamman da ya yi da LEADERSHIP A YAU a kwanan nan, inda ya kara da cewa, ba laifi ba ne idan a yanzu sun nemi afuwar Jonathan bisa irin tawayen da su ka yi ma sa a wancan lokaci, amma Buhari ya zo ya watsa mu su kasa a gwiwa.

“Dole mu ji kunyar sa (Jonathan), har ma watakila wataran mu ba shi hakuri, domin mun gaya ma sa maganganu a kan abinda ya kasa yi, sai ga wanda ya gaje shi (Buhari) ya gaza kai wa shi,” in ji shi, ya na mai karawa da cewa, “Saboda haka dole a ba shi hakuri, domin ya yi abinda wannan ya yi. Wajen maganar tsaro ga ta nan ta kara lalacewa.

“Daga Boko Haram an taso kisan kiyashi da sace mutane, a na kashe ma na mutane kamar kiyashi, amma daga alama kuma an fi damuwa da inda a ka kashe mutum daya; dan gata, za ka ji surutu iri-iri, kamar kwanan nan da a ka kashe wata mata. Wacce irin makyarkyata ce gwamnatin ba ta yi ba; ta na bada umarnin a kai sojoji? Amma mu nan a na kashe mutane, kisan kiyashi. Ko ta’aziyyar ma ba a yi.”

Farfesa Ango ya jaddada cewa shi ba mutum ne wanda ya ke ganin gaskiya ya rufe bakinsa ya yi shiru ba komai kusacinsa da abin, inda ya tuno da cewa, “Ina cikin wadanda su ka kafa PDP, mu goma. Allah ya ji kan Abubakar Rimi da su Solomon Lah da sauransu tare mu ka kafa ta. Mu mu ka bada kundin tsarin mulkinta da manufofinta.

“Amma tun 2003 na watsar da harkar jam’iyya na dawo gida na zauna. Obasanjo abokina ne; a nan gidan nawa a ka tsara harkar tsabensa (a 1999). Saboda haka da mu ka ga ya kasa yin wasu abubuwa, musamman ni ta gefena; harkar gona, mu ka fara fada da shi har na bar gwamnatinsa a 2003. Daga nan ma na bar maganar jam’iyya gabadaya.

“To, saboda haka abinda mu ke gani shi ne, ita jam’iyyar PDP ta kasa. Shi ya sa mu ka yake ta a 2015. To, sai ga wata wacce mu ke mafarkin za ta yi abin kirki (APC), ita ma gwamma jiya da yau. Saboda haka mu na nan mu na sa rai dai ku matasa za ku fito da wata jam’iyya.”

Ya kara da cewa, “Ni ne jagoran Buhari ya kayar da Jonathan a 2015. Sai dai idan ka san yawancin mutane mantuwa ne da su, musamman masu neman fada da na abinci. Amma idan ba haka ba (an san) ni na yi jagora a kayar da Jonathan a wancan zabe.

“Buhari ya yi shekara 12 ya na neman shugabancin kasar nan ya kasa samu, amma da mu ka zo mu ka taru, ya samu zabe, saboda mu na sa ran cewa zai yi wani abin gani, inda abinda ya sa mu ka matsa wa waccan gwamnati, zai kau da jiki daga irinsu, domin a dawo a fuskanci abubuwan da mu ke kishi wadanda ya kasa yi ko ya ki yi.”

Da ya ke magana kan abubuwan da ya ke zargin gwamnatin APC ta gaza aiwatarwa, ya ce, “abubuwan da Buhari ya kasa yi ba su da iyaka. Talauci ya karu a Arewacin kasar nan, babu ilimi, babu magani a asibiti, ba hanyoyi, ga makudan kudade da a ke kashewa mun san inda su ke zuwa; kudancin kasar. A nan Arewa a ka ba shi kuri’a kashi 81 cikin 100, amma nan ne kuma ya watsar.”

Da ya tabo batun ayyuka da gwamnatin Buhari ta kaddamar, musamman a Arewacin Najeriya, farfesan ya ce, “jirgin kasa Jonathan ne ya yi, ba Buhari ya yi ba.”

Ya kuma karyata yunkurin gwamnatin na bude tashar jirgin ruwa ta Baro da aikin hako mai na Bauchi da Shugaba Buhari ya kaddamar da su.

“Ba mu gani ba tukunna. Rabu da cewa shugaban kasa ya je an yi bikin budewa a kai. Sai mun gani a kasa tukunna. Maganar yashe ruwan teku ma, Umaru Yar’Adua shi za mu jinjinawa a kan wannan. Shi ya yi kokarin a kara fadada Kogin Neja yadda manyan jirage daga teku  za su shigo mu samu tashar jirgin ruwa mu ma a cikin Arewa.

“Sau da mu ka duba kasafin kudin da Buhari ya yi na 2016 mu ka ga ko Kwabo ba a saka ba. Sai da mu ka je wajen su Saraki, su Dogara (tsofaffin shugabannin Majalisar Dokoki na kasa), sannan su ka yi wani abu a kai. Har yanzu maganar samar da hasken wutar lantarki na Mambila surutu kawai a ke yi, sai kwanan nan ne a ka ga dan wata alama wai cewa za a yi.

“Kamfanin mulmula karafa na Ajakuta ma an watsar da shi. Babu wani abu da wadannan mutane su ka a cikin shekara hudu, sai kara ja baya da kasa ta yi, musamman mu a nan Arewa,” a cewarsa.

Kan batun zargin da a ke yiwa farfesan kan wata boyayyiyar ajanga ka kashin kansa, wacce ta sanya ya ke sukar gwamnati, ya mayar da martani da cewa, “Ba na neman mukamin shugaban kasa kuma ba su taba ganin na nemi a bai wa wani yarona aiki ba. Ina da su sun gama digiri, amma ban nemi komai daga gare su ba. Saboda haka ba ni da wata bukata sai abinda na ke kishi na akidar da na rayu a kai, domin iyayen da su ka raya mu sun koya ma na kishin kasa da yankin Arewa.”

A yayin da mu ka tambaye shi kan ko a matsayinsu na dattawa sun dauki wani mataki na ankarar da gwamnatin korafinsu, sai dattijon ya ce, “babu abinda ba mu yi ba na ganin gwamnati nan ta gyara. Maitama Sule ne shugabanmu kafin na karba daga hannunsa bayan ya rasu. Shi mu ke sa wa a gaba mu tsara shawarwari ga shugaban kasa. Duk da tsufansa haka Maitama Sule ya ke zuwa ya kai shawarwarin da mu ka cimma, amma babu abinda a ka yi har ya mutu. Kuma bayan mutuwarsa ma ba a yi komai ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!