Connect with us

RAHOTANNI

Mun Samar Da Sabbin Dabarun Murkushe Boko Haram, Cewar Sojoji

Published

on

A jiya Lahadi ne Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewar ta fitar da sabbin dabarun yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram wadanda suke kai hare-hare a wasu yankunan jihar Borno.

Manjo Janar Olusegun Adeniyi, Kwamandan Theater na Operation Lafiya Dole shine ya shaida hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘yan jarida kai ziyara kananan hukumomin Magumeri, Gubio da Kaga da suke jihar ta Borno.

Kamfanin Dillacin Labarai ta kasar nan (NAN) ta habarto cewar, Manjo Janar Adeniyi ya kuma yi jawabi mai ratsa zukata ga sojojin barikin 5 Brigade Battalion kana ya kuma zanta da al’umman yankunan da ya ziyarta.

Sai dai kuma ya musanta labaran da suka bazu na cewar sojoji sun janye jami’ansu a yankunan da Boko Haram suka kaddamar da hare-hare a kwanakin nan da suka wuce, ya ce babu wani zance makamancin hakan jami’ansu suna kan gudanar da aiyukansu yadda ya dace.

Kwamandan ya yi batun cewar sun samar da sabbin dabaru da tsare-tsaren yaki da ‘yan Boko Haram yanzu haka, har ma ya ce sun samar da wani tsari na ‘Super Camp’ da zai tabbatar da dakushe mayakan Boko Haram da kuma kare rayukan jami’an soji a lokacin da suke fafatawa da mayakan, kana sabon tsarin wata dabarace da sojojin zasu ke sintiri don hana ‘yan ta’addan sakat.

“Yan Nijeriya suna da bukatar fahimtar cewar lallai sojoji ba su janye daga Magumeri, Gubio ko wani yanki na jihar Borno da arewa maso gabashin Nijeriya ba.

“Rundunar soji ta samar da wani tsari a yanzu a maimakon sojoji suke zama wuri guda, an samar da sojojin sunturi wadanda zasu ke sunturi don yaki da ‘yan ta’adda don tabbatar da kare al’umomi da hanyoyi daga ta’asar mayakan,” A cewar shi.

Ya kara da cewar hakan zai baiwa jami’an soji damar kasancewa a kowani wuri da hana wa ‘yan ta’addan damar motsawa duk inda suke so, kana hakan zai taimaka sosai wajen rage kaifin ta’addanci.

“Eh gaskiya ne ‘yan ta’addan sun kai hari a kananan hukumomin Magumeri da Gubio; sai dai babu wani soja ko farar hular da suka rasa rai a wannan harin, illa dai mamban Cibilian Joint Task Force (CJTF) guda ya rasa ransa da kuma wasu mutane shida da suka gamu da raunuka, walau ko harbin harsasai ko kuma a kokarin arcewa suka gamu da raunukan.

“Kananan hukumomin Gubio da Magumeri suna karkashin kulawar sojoji sannan jama’a sun dawo gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Sannan za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyar jama’a hadi da baiwa jama’a dukkanin tsaron da ta dace,” A cewar shi.

Manjo Janar Adeniyi ya kuma kara da cewar rundunar sojin kasa ta kuma samar da karin motoci da wasu karin kayan aiki wa jami’anta domin tabbatar da kakkabe aiyukan ‘yan Boko Haram.

Sai kuma ya yi kira ga jama’a da su kasance masu taimaka wa sojoji wajen yaki da ‘yan ta’addan, kana ya kuma basu tabbacin sojoji na kare musu yankunansu.

Da yake jawabinsa shi kuma, Birgediya Janar Sunday Igbinomwahhia, Kwamandan Garrison na bataliya ta 7, ya ce sojoji masu sunturi a karkashin Super Camp Operation an samar da sune da zimmar su yi aiki babu dare babu rana na tsawon awannin 24 domin tabbatar da tsaro a yankunan Maiduguri da Damaturu.

Manema labaru sun tabbatar da cewar al’ummar Magumeri da Gubio sun dawo gudanar da harkokinsu na yau da kullum lafiya, kama daga kasuwanci da kuma harkokin noma da sauransu biyo bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kai musu.

Idan za ku iya tunawa a ranar Juma’a ne dai LEADERSHIP A YAU ta kawo muku rahoton da ke cewar kananan hukumomin Magumeri da Gubio sun gamu da munanan hare-hare na ‘yan Boko Haram wadanda suka kaddamar da jerin hare-hare tun daga ranar Laraba har zuwa kashegarin ranar Alhamis suna cin karensu babu babbaka, inda suka rusa gidajen jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!