Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sin Za Ta Mayar Da Martani A Hankali Kan Cin Zarafin Cinikin Amurka

Published

on

Yau gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani bayani mai taken “Kasar Sin za ta mayar da martani a hankali kan cin zarafin cinikayyar da Amurka ta yi mata”, inda aka yi nuni da cewa, kwanan baya Amurka ta sanar da cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin kasar Sin da ake shigo da su kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 300, kasar Sin ta ga cewa tilas ne ta dauki hakikanin matakin mayar da martani bisa dokokin kasar da abin ya shafa da ka’idojin kasa da kasa, lamarin da ya sa wasu Amurkawa wadanda ke da ra’ayin nuna karfin tuwo sun yi fushi matuka saboda suna ganin cewa, idan Amurka ta kara sanya haraji kan kayayyakin wata kasa, dole ne ta amince da matakin Amurka, bai kamata ba ta yi adawa, hakika wannan tunanin fin karfi na nacewa ga bangaranci da ba da kariya ga cinikayya zai yi illa ga dokokin kasa da kasa da kuma tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa.

A cikin bayanin, an jaddada cewa, haka kuma ya dace a gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, a don haka abokan cinikayyarta a fadin duniya na adawa da takaddamar cinikayyar da ta tayar.
Kan wannan batun, har kullum kasar Sin ta nace kan matsayin, wato ba ta so ta yi yakin cinikayya, amma ba ta jin tsoron yakin ko kadan, idan ta ga dama, za ta mayar da martani, kasar Sin tana son daidaita matsala bisa tushen daidaito da martabar juna, amma idan aka matsa lamba, to, ba za ta ba da kai bori ya hau ba. (Mai Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: