Connect with us

RAHOTANNI

Iyalan Ogunsola Sun Nemi Adalci Kan Kisan Dansu

Published

on

Iyalan Ogunsola da ke yankin Owode Egba a jihar Ogun, wanda aka yi zargin dansu mai suna Isamaila Mukaila Ogunsola an kashe shi a gonar ogansa, sun kirayi shugaban ‘yan sanda na kasa, Muhammad Adamu da ya taimaki iyalan wajen samun adalci kan kisan dan nasu.

Har-ila-yau, iyalan sun kuma bukaci gwamnan jihar, Dapo Abiodun, da ya tabbatar ya bi dukkanin matakan da suka dace don ganin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun kada su rufe zancen ba tare da an yi adalci ba.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, mahaifin wanda aka kashen, Mukaila Ogunsola, ya ce ko kadan ba su ji dadin iri matakan da tawagar ‘yan sandan da ke gudanar da bincike kan kes din kisan ke yi, wanda a cewarsu babban wanda ake zargi kan kisan Segun Adekoya an sake shi tunin.

Mukaila yayi zargin cewar kawo yanzu ba su da kwarin guiwar samun adalci daga jami’an da ke gudanar da bincike kan wannan zancen, yana mai neman wadanda abun ya shafa da su gudanar da dukkanin abun da ya dace domin tabbatar da an yi adalci kan wannan kisan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!