Connect with us

LABARAI

Kano Gari Ne Da Masu Laifi Ba Su Da Mazauni A Cikinta – Wakilin Dukiya

Published

on

An bayyana jihar Kano da cewa gari ne na arziki mai kima da karamci ba’a kasarnan kadai ba,harma a nahiyar Afirka da Duniya baki daya.

Tsohon shugaban kungiyar ’yan canji na jihar Kano, Alhaji Yusuf Wakilin Dukiya, ya bayyana haka a yayinda yake wani martani bisa wani hasashe da wata jarida ta yi na danganta Kano da cewa ta na tattara ’yan ta’adda.

Cikin bacin rai Alhaji Yusuf Wakilin Dukiya ya ce abin rashin jin dadine da rashin kyautawa wani ya danganta Kano da wannan kalma marama dadin fada ko ji.Kowa yasan duk mstsalarda ta taso a kasarnan idan ta tunkaro Kano za’a kauda ita dan haka ba wani abu na rashin kyautawa da yake tasiri a Kano saboda kullum dare da rana a cikin addu’a ta neman kariyar Ubangiji suke.

Alhaji Yusuf wakilin Dukiya wanda dan asalin jihar Kanone daga kasar Dawakin kudu wanda yake zaune a kwaryar birnin Kano Dala ya ce rashin kyautawane wani yazo ya ce Kano matattarace da tara yan ta’adda wannan bai ma kamata a danganta Kano ba

Alhaji Yusuf Wakilin Dukiya yayi kira ga al’ummar Kano su cigaba da jajircewa akan addu’oi da suke kullum na neman kariya daga Allah akan duk wata matsala da za ta taso da kuma bunkasar arzikinta a kowane yanayi wannan kokari da ake a Kano na neman taimakon Allah a kowane yanayi shi yasa ta zama tafi kowane gari tashe da daukaka ake mata kirari da cewa ko  da me ka zo an fi ka.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: