Connect with us

RIGAR 'YANCI

Za Mu Cigaba Da Kare Rayukan Al’ummar Kankara Bakidaya – Shugaban ’Yan Sunturi

Published

on

Shugaban ’yan kungiyar sunturi na karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, Alhaji Aminu Koshe Kankara, ya bayyana cewar, shi da abokan aikinsa na kungiyarsu ta ’yan sunturin karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina za su iyakar kokarinsu a wajen kare rayukan al’ummar karamar hukumar Kankara da dukiyoyinsu a jihar Katsina da kewayanta bakidaya.

Shugaban kungiyar ’yan sunturin na karamar hukumar Kankara, Alhaji  Aminu Koshe Kankara, ya yi wannan tsokaci ne jim kadan bayan da kungiyar ta ’yan suntiri na wannan yankin na Kankara su ka kammala taronsu na mako-mako da su ka saba yi a duk karshen mako kuma taron ya gudana ne a ranar Juma’a da ta gabata.

Sannan shugaban na ’yan sunturi ya cigaba da cewa babu shakka zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari a karamar hukumar Batsari ya kara mu su kwarin gwiwa a bisa bayanansa na cewar gwamnatinsa za ta yi iyakar kokarinta a wajan kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane da ’yan ta’adda ke yi  a arewacin Najeriya da sauran wadansu jihohin da irin wadannan al’amarin ke faruwa, in ji shi, da fatan Allah ya yi ma sa jagoranci a wajen gudanar da wannan al’amarin.

Shugaban ’yan sunturin ya kara da cewa ko a garin Kankara ma sun gani a kasa, a cewarsa, domin kuwa kantoman riku na karamar hukumar Kankara, Hon. Alhaji Anas Isah Kankara, ya rarraba jami’an tsaro a kan hanyoyin zuwa wadansu kauyukan da ke wajen Kankara da kewayenta, domin kare lafiyar al’ummar Kankara da dukiyoyinsu a game da kashe-kashen ’yan ta’adda ke yi da garkuwa da mutane a garin na Kankara da kewayanta, al’amarin da ya sanya a ka samu saukin wannan al’amari a garin na Kankara.

Ya kara da cewa, da fatan Allah ya cigaba da ba shi nasarorin gudanar da  jagorancin jama’ar wannan yanki na Kankara a cigaba da jawabinsa a gurin taron uban kungiyar ta ’yan sunturin karamar hukumar, Alhaji Musa Koshe ya ce, wajibi ne shugaban kungiyar Alhaji Aminu Koshe shi da sauran mambobin kungiyar su tsaya tsayin-daka domin kare lafiyar al’ummar wannan yanki na Kankara da dukiyoyinsu da jihar Katsina bakidaya.

Sannan ya yaba wa gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a kokarinsa na kawar da miyagun ayyuka a jihar da kewayanta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!