Connect with us

LABARAI

Ana Ci Gaba Da Dambarwa Kan Motocin Yakin Da Aka Shigo Da Su Nijeriya

Published

on

Ana ci gaba da samun dambarwa dangane da hakikanin mamallakin motocin yaki masu sulke guda shida da jami ‘an tsaron Nijeriya suka kama a kan iyakar kasar da Kamaru da ke garin Konkol na karamar Hukummar Maiha ta jihar Adamawa.

Majiyoyi sun ce, an yi nufin isar da motocin yakin ne ga hukumomin Jamhuriyar Nijar, amma kawo yanzu mahukuntan kasashen Nijeriya da Kamaru ba su fayyace ainihin mamallakin motocin ba.

A yayin da bayanai ke cewa, gwamnatin Nijar ce mamallakiyar motocin yakin, wasu rahotanni cewa suka yi, na Kamaru ne, yayin da wasu majiyoyin suka danganta motocin da kasar Amurka.

Tuni Kwamandan bataliyar sojoji ta 23, S.G. Mohammed ya mika motocin yakin ga Hukumar Hana Fasa Kauri wato Kwastam, reshen jihar Adamawa da Taraba.

Hukumar Kwastam ta shirya gudanar da taron manema labarai kan wannan dambarwa a birin Yola, amma daga bisani aka soke taron saboda an mika batun ga hukumomin birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu, shugaban Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya bayar da umurnin gudanar da bincike kan al’amarin.

Majiyar Kwastam ta ce, an kama motocin ne saboda rashin takardun izinin safarar su zuwa wata kasa, yayin da wasu bayanan ke cewa, gwamnatin Amurka ce ta yi wa sojojin kasar Nijar kyautar motocin.

A cewar wasu rahotanni, hukumomin Amurka sun yi mamaki game da kame motocin, inda suka dora laifin aukuwar haka kan rashin musayar bayanai tsakanin jami’an tsaron Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: