Connect with us

WASANNI

Eric Cantona Zai Karbi Kyautar Shugaban UEFA Ta Bana

Published

on

Tsohon dan wasan gaba na Manchester United, Eric Cantona zai karbi kyautar shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Turai saboda gudunmawar da ya bayar ta inganta rayuwar wasu mutane. A ranar Alhamis mai zuwa ne, tsohon dan wasan mai shekara 53 wanda ya buga wa Faransa wasanni 45, zai karbi wannan kyauta a birnin Monaco.

Shugaban hukumar UEFA, Aleksander Ceferin ya gamsu da irin aikin da Cantona ke yi tun bayan ritayarsa daga fagen tamaula.

A shekarar 1997 ne, Cantona ya yi ritaya bayan ya cika shekara 30 da haihuwa, yayin da ya karkata hankalinsa kan harkar kwallon yashi da kuma fina-finai, sannan kuma yana bayar da gudunmawa ta fannin agaza wa mabukata.

Tsoffin ‘yan wasa irin su David Beckham da Johan Cruyff da Bobby Charlton da Franz Beckenbauer da Bobby Robson da kuma Paolo Maldini sun taba lashe irin wannan kyauta ta shugaban hukumar UEFA.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: