Connect with us

LABARAI

Hadarin Gusar Da Budurcin Mace Ya Na Da Yawa – Yaro Coca-cola

Published

on

Har kullum malamai suna ta bayani a kan hadurran da ke tattare da mutum ya kawar da budurcin macen da ba tashi ba, saboda haka aji tsoron Allah a guji kusantar aikata hakan. Ba kuma wani abu ne yake kawo wasu ke aikata hakan ba face rashin tsoron Allah da jefa kai a cikin fituntunu irin na neman Duniya.
Masu kuma fakewa da suna aikata hakan ne a lokacin da suka yi shaye-shaye hankulansu suka bata, su ma ya kamata su ji tsoron Allah domin sam wannan ba zai taba zama karbabben uzuri ba, saboda ai shi kansa shaye-shayen din haramun ne Allah Ya hana, don haka duk wanda ya sha wa kansa abin da zai iya gusar masa da hankali har ta kais hi ga aikata wata barna, to sunansa mabarnaci, kuma hukuncin duk da shari’a ta tanada wa wanda ya aikata laifin nan yana nan a kansa.
Abin kunya akan sami ma wasu da za ka ga da jikokinsu ne, a cikin jikokin ma kananan jikoki, wadanda sunansu ne kadai mace, amma ba da ma ma’anar mace abar sha’awa ko jin dadi ba. a gaskiya idan har mutane za su ji tsoron Allah su kwauracewa irin wadannan abubuwan za a zauna lafiya.
Kuma duk da cewa tsarin mulkin Nijeriya ya baiwa duk wani wanda ake tuhuma da aikata laifi ya dauki Lauyan da zai kare shi, domin ba a tabbatar da laifi a kan mutum sai an tuhume shi, shari’a ta tabbatar da aikata laifin nan na shi. To a nan yana da kyau su ma Lauyoyin nan da Allah Ya tsaga masu abincinsu ta wannan hanya da su ji tsoron Allah a kan wannan aikin na su. kamar yanda tsarin Musulunci ya tanada cewa ga laifi an ganshi kuru-kuru, amma sai hukuma ita ce za ta yi hukunci a kan wannan laifin da aka aikata.
Wata babbar nasarar kuma ita ce, babu wani nau’in laifi da Allah bai tanadi hukunci a kan wanda ya aikata shi ba, saboda haka idan da alkalan za su leka su duba a ga hukuncin da Allah Ya tanada a kan masu aikata irin wannan laifi a zartas masu, tabbas shi ma da an sami lafiya. Sau da yawa neman abin Duniya ne ke kai wasu fadawa a cikin aikata irin wannan laifin, ko da karamar mace ce, ko namiji ko karamin yaro duk za ka taras wani abin Duniya ne ake nema da aikata hakan, wanda a karshe sai ka taras Duniyar ma ba ta samu ba an kuma aikata mummunan laifin da za a ji kunya a Duniya a kuma je Lahira a hadu da azabar Allah a kansa. Wa’iyazu billahi da fadawa a cikin irin wadannan laifukan.
Muna kuma fata shari’a za ta rika gaggautawa wajen zartas da hukunci a kan masu aikata irin wadannan laifukan. Ka da a yi ta jan Magana sannu a hankali har abin ya zo ya watse tare da hadin kan iyayen gidan masu aikata laifin ko mu ce bokayensu da suke dora su a kan aikata irin wadannan munanan laifuka.
A halin yanzun akwai ma kungiyoyi da yawa masu rajin kare hakkin dan adam musamman masu kokarin ganin sun tsayawa wadanda irin wannan abin ya shafa, to ya kamata ne a ba su hadin kai a taimaka mu su.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: