Connect with us

LABARAI

Hukuncin Bashin Dala Biliyan 9.6: Laifin Gwamnatin Yar’Adua Ne – Gwamnatin Tarayya

Published

on

  • Buhari Ya Umarci EFCC, NIA Da IGP Su Binciki Muna-Munar Da A Ka Yi

Gwamnatin tarayya ta alaqanta aikin kwangilar da aka zartas da hukuncin biyan dala Bilyan 9.6, kimanin naira Triliyon 3.5 a kan gwamnatin tsohon Shugaban Qasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, saboda shiga yajejeniyar da ta yi a shekara ta 2010, gabanin rasuwarsa.
Gwamnatin ta tarayya ta ja daga da musu a kan hukuncin da a ka yanke a kan bashin, inda ta ke iqirarin cewa ba ta amince ba.
Ta kuma ce Shugaba Buhari ya umarci hukumomin EFCC, NIA da babban sufeton ’yan sanda na qasa da su fara bincikar duk wata muna-munar da ke cikin kwangilar da ba ta yiwu ba.
Gwamnatin ta ce, sam kamfanin da a ka bai wa kwangilar na Pocess and Industrial Developments Ltd. (P & ID) bai ma yi kwangilar ba.
Gwamnatin ta yi waxannan bayanan ne a wani taron manema labarai na haxin gwiwa a Abuja, wanda Ministan sadarwa da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, tare da Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), da Ministar kuxi, Zainab Ahmed da kuma gwamnan babban bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefeile, su ka gabatar.
Mohammed ya ce, “mun gayyace ku a nan ne yau domin mu yi maku bayani a kan hukuncin da kotun Ingila ta zartar a kwanan nan, inda ta bai wa kamfanin Process and Industrial Developments Ltd. (P & ID), hukuncin damar riqe kadarorin Nijeriya da qimarsu ya kai Dalar Amurka bilyan 9.6 a bisa wata kwangila da a ka qulla a tsakanin kamfanin da ma’aikatar albarkatun man Fetur a shekarar 2010.
“A gurguje za mu ba ku labarin abin da ya wakana da kuma halin da a ke ciki gami kuma da abinda gwamnatin Nijeriya ke yi domin dakatar da qwace ma ta duk wata kadarar tata.
“Mu na sa ran a lokacin da mu ka gama yi mu ku waxannan bayanan, kafafen yaxa labarai za su fahimci yadda lamarin ya ke sosai, ta yadda za su sanar da ‘yan Nijeriya gaskiyar abin da ya ke gudana.
“Hukuncin da a ka zartas a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta, 2019, ya shafi abinda ya wakana ne a kan wata kwangila da ba a aiwatar da ita ba, wacce a ka qulla ta a shekarar 2010 tsakanin ma’aikatar albarkatun man Fetur ta qasa da kamfanin. Ku yi la’akari da yarjejeniyar nan da a ka qulla ta samar da Iskar gas na tsawon shekaru 20, wacce a ke iqirarin an qulla da kamafanin P&ID a shekarar 2010, waccce kamfanin bai yi aikin ba kamar yadda a ka yi yarjejeniya da shi.”
Malami kuma ya ce tun farko an shirya kwangilar ce ba ta yanda za ta yi aiki ba. “mu na bisa binciken duk wata muna-muna da a ka tafka a kan aikin.”
Minister kuxi, Uwargida Zainab Ahmed ta ce, sam wannan hukuncin ba zai tabbata ba, kuxinsa ya kai Naira triliyon 3.5, adadin kasafin kuxinmu na shekara guda bakixaya.
Gwamnan babban bankin qasa ya ce, “kamfanin na P&ID bai zuba jarin ko sisi ba a cikin qasar nan, ya qalubalanci kamfanin da ya kawo hujjarsa a kan hakan.”
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: