Connect with us

RAHOTANNI

Jibril Diso Ya Zama Makahon Farfesa Na Farko A Jami’ar Bayero

Published

on

A tarihin Nijeriya, wannan ne karo na farko da aka taba samun Makaho wanda ya kai kololuwa, wato Shehun Malami a bangaren matakin ilimin, mai suna Farfesa Jibrin Isah diso. Kazalika, Farfesa diso, Malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan mutum ne da ya jima yana yin gwagwarmayar rayuwa, musamman a bangaren sha’anin ilimi da kuma koyar da shi. Sannan Farfesan, shi ne mutum na farko da a tarihin Kano; wanda ya fara rike mukamin Mai baiwa Gwamna shawara a bangaren sha’anin Masu Bukata ta Musamman a Kano, a zamanin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau.
Kamar yadda tarihi ya nuna, an haifi Farfesa Jibrin Isah diso, a shekarar 1957, a Unguwar diso da ke cikin Birnin Kano. Ya fara makarantar Firamare dinsa a dandago, ya kuma kammala a shekarar 1969. Daga nan ne, sai Shehin Malamin ya wuce zuwa makarantar Sakandire ta Gwale G2, sannan ya yi koyarwa a makarantar masu bukata ta musamman a Tudun Maliki, sai ya sake wucewa zuwa makarantar Sakandire ta Wudil, daga nan ne kuma ya samu nasarar shiga Jami’ar Bayero da ke Kano, a matsayin mai koyarwa na wucin gadi.
Har ila yau, sakamakon irin kalubalen da ya samu na kasancewarsa a matsayin mai larura ta idanu, amma sai ya dage tare da nuna sha’awarsa ta ci-gaba da sha’awar wannan aiki na koyarwa, sakamakon gwazonsa yasa aka dauke shi a matsayin cikakken Ma’aikaci, ya tashi daga Maaikacin Maaikatar ilimi zuwa Maaikacin Jamiar Bayero da ke Kano (BUK).
Haka zalika, a ranar Lahadin da ta gabata ne, ‘yan’uwa da Abokan arziki suka shirya wa Farfesan wata gagarumar liyafa, domin taya shi murnar samun wannan nasara tare da jinjina wa kwazonsa na kasancewarsa guda kuma na farko a yankin Arewa da ma Nijeriya bakidaya, da ya fara samun irin wannan matsayi ko nasara.
Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, Shugaban Tsangayar Ilimi ta Jamiar Bayero (BUK), shi ne ya kasance a matsayin babban bako mai jawabi a wurin wannan biki na taya Farfesa diso, murna. Kazalika, ya bayyana nasarar Farfesan a matsayin wani babban kalubale ga sauran masu lalurar Ido ko wata gaba, har ma da sauran masu lafiyar. “Wannan ba karamin babban kalubale ba ne, yau a ce ga mai lalurar Ido ya kai matakin Ilimin kololowa a Jami’a (Farfesa), hakan na tabbatar da cewa, kowane irin abu dan Adam ya sanya gaba, ko shakka babu Allah zai taimake shi; ya samu”, in ji shi.
Farfesa Ali, ya ci gaba da bayyana cewa, babu wanda zai iya zama Farfesa, har sai ya shiga Jami
a ya yi Digiri na daya da na biyu kuma na uku, sannan ya yi rubuce-rubuce tare da bayar da gudunmawa ta Ilimi, kana kwararru su duba rubuce-rubucen da kuma gudunmawar da ka bayar din, kafin su kai ga yarda da wannan matsayi naka na cancantar zama Farfesa. “Alhamdulillahi! Jibrin Isah diso, yau kai ne Farfesa na farko a Nijeriya cikin kaf cikin masu lalurar Idanu.”
Har wa yau, Farfesa Tijjani ya ci gaba da yin karin haske; inda ya bayyana cewa, Jamiar Bayero na da shashi na musamman ga masu neman Ilimi na musamman ga masu bukata ta musamman, sannan akwai kwararrun Malamai masu koyarwa da kuma dukkanin kayan aikin da ake bukata. Saboda haka, wannan na nuna mana cewa, lallai nakasa ba ta hana neman Ilimi ko samunsa, in dai har da kyakkyawar niyya da kuma jajircewa, duk dai da cewa, Farfesa diso shi dama dan Baiwa ne, kuma abin misali a cikin alumma, a cewar tasa.

Shi ma a nasa Jawabin, Farfesa Jibrin Isah diso, ya bayyana farin ciki da kuma godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, da ya yarda da wannan lamari nasa na zama Farfesa. Haka kuma, ya sake mika godiyarsa ta musamman ga Malam Kabiru Haruna, da Jami’ar Bayero da ke Kano, da kuma sauran daukacin Ma’aikatanta da kafofin yada labarai da hada da Leadership A Yau, da kungiyoyin alumma na gida da na waje, kamar DIFD da sauran makamantansu.
Har ila yau, diso ya kara da cewa, babu shakka wannan nasara na tare da babban kalubale, musamman idan aka yi la’akari da yadda kayan karatunmu ke da matukar tsada, tun daga kan na’urar Kwamfuta wadda kudinta ya kai kimanin Naira 700, wadda da ita ne za a iya samun damar shiga yanar gizo (internet).
“Bayan kammala karatuna a Jami
ar Bayero, na kuma samu nasarar wucewa zuwa Jami’ar Birmingham da ke kasar Ingila, inda na yi Digirina na uku a fannin Falsafal Ilimi (Philosophy) wanda ya ba ni damar zama Farfesa.

Haka kuma a karshe, ya yi kira tare da jan hankali ga sauran masu bukata ta musamman da cewa, barace-barace, ba zai taba zama mafita ba, idan mutum zai iya yin wani abu na sana’a, to fa haramun ne ya yi bara.
Wakazalika, wannan taron walima ya samu halartar dimbin jama’ar da ke Unguwar diso, cikin karamar Hukumar Gwale, karkashin jagorancin Mai Unguwar ta diso Malam Tijjani Bello diso, da kuma sauran al’umma daga sassa daban-daban na Jihar Kano da ma wajenta, ciki har da Abokanan karatunsa, dalibai, ‘Yan kasuwa, Shugabanni da kuma Malaman Jami’a.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: