Connect with us

LABARAI

KEDCO Ta Mayar Wa TCN Martani Kan Rashin Bada Wutar Lantarki

Published

on

Kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano ta KEDCO ta mayar da martani game da jingina matsalar mata laifin gazawar samar da wuta da hukumar tunudo da wuta ta TCN ta yi mata.
Mai magana da yawun Kamfanin na KEDCO, Ibrahim Sani Shawai ya shaida wa manema labarai cewa KEDCO ba za su ita biyan kudin lantarki cikakke ga TCN ba, sakamakon suma basa samun cikakken biyan kudin wuta daga abokan huldarsu.
Ya kara da cewa, dage wutar lanlarki da TCN ya yi wa KEDCO a manyan layukanta guda biyu saboda ya bukaci sai an biya kudin wutane 100 bisa 100 ita ma KEDCO bata karbar haka a wajen abokan huldarta a kowane wata.
Alhaji Ibrahim Sani Shawai ya ce, haka nema yasa a wani lokaci akan yi tsarin karba-karba wajen bada wutar lantarku domin kowa ya amfana kuma a tabbatar da daidaito na adalci da amana a tsakanin abokan huldarsu dake a jihohin Kano da Katsina da Jigawa.
Shawai ya jaddada irin kokari da KEDCO take wajen ganin ta samarda wuta domin biyan bukatun al’umma. Matsalolin da ake samu ma a yanzu yana da dangantaka ne da wasu yan matsaloli na ruwan damina daya jawo da kuma yar takaddama data taso tsakaninsu da kanfanin tunkudo wutar ta TCN da ake kokarin warwarewa.
Tun farko dai TCN ta zargi rashin samun wutar lantarki a shiyyar da KEDCO ke bayarwa da cewa gazawar KEDCO ne.
Shugaban TCN, Alhaji Usman Gur Muhammad ya ce, akwai kamfanoni da suke hulda dasu takwarorin KEDCO a wasu sassa na kasar nan an bijiro musu da matsalolinsu sun kuma gyara amma KEDCO sun gaza gyara nasu shi yasa suka dage su daga wasu hanyoyi na samun don gargadi, amma sai ya zama kuma wanda ake basun ma basa bayarwa yanda yakamata ana ta kukan rashin samun wuta a Kano da Katsina da Jigawa dan haka TCN ke ganin kamar da gangan KEDCO take domin su batawa NTC suna.
Sai dai wannan rashin fahimta da aka samu har yake jawo karancin bada wutar lantakin jama’a da dama sunfi dorawa KEDCO nauyin hakan saboda yawanci basu ma san matsayinda TCN take takawa a harkar bada wutar lantarki ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: