Connect with us

RIGAR 'YANCI

2023: el-Rufai Ya Dace Ya Zama Shugaba Nijeriya, Cewar Magani-Sai-Da-Gwaji

Published

on

An bayyana gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmaed El-Rufa’I da cewar shi ne wanda ya kamata al’ummar Nijeriya ya kamata su zaba, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shugabancin Nijeriya a shekara ta 2023.
Shugaban karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim [ MAGANI SAI DA GWAJI ] ya bayyana haka a lokacin da uwar gidan gwamnan jihar Kaduna ta kawo ziyarar godiya ga Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke birnin Zariya.
Injiniya Aliyu Idris ya kare batunsaa da cewar, duk wanda ya san yadda gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’I ya karbi jagorancin jihar Kaduna, ya san ya karbi jihar da matsaloli ma su yawan gaske, amma, a cewarsa, ya tunkari matsaloli, musamman na zaman lafiya, ya kuma sami nasara a
kansu.
A kan haka ne ya ce, yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi tsaye, na ganin ya tabbatar da tsaro a wasu jihohi da a ke kamfar tsaron, haka ma, in ji Injiniya, gwamna El-Rufa’I ya tunkari matsalolin tsaro a jihar Kaduna, ya kuma sami nasarori ma su yawan
gaske.
Game da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar Kaduna da kuma samar da daburun zamani na ayyukan gwamnati kuwa, Injiniya Idris ya tabbatar da cewar, al’ummar jihar Kaduna sun fara gani a kasa, tun a shekarar da ta gabata, na ayyukan ci gaba da gwamnan jihar Kaduna ya aiwatar a fannonin ilimi da kiwon lafiya da sauran bangarori da ma su yawan gaske da mafiya yawan al’ummar jihar Kaduna ba su gani a shekarun baya ba.
Sauran dalilan da Magani said a gwaji ya ce gwamna El-Rufa’I ya fi dacewa a ya gaji Shugaba Buhari sun ne, yadda gwamnan jihar Kaduna ya naxa kwararrun da suka dace a matsayin kwamishinoni, wannan alamu ne da suka nuna gwamnan jihar Kaduna shugaba ne da ya ke tunanin waxanda su ke mulka.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: