Connect with us

LABARAI

Ambaliyar Ruwa A Jigawa: Gwamnati Ta Kashe Naira Miliyan  2.7 Wajen Gyaran Kogin Hadeja

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ya zuwa yanzu ta ce ta kashe naira miliyan 2.7 wajen gyaran ciyawa da ta rufe kilomita 15 a jikin kogin Hadeja da ke karamar hukumar Guri a jihar. Jami’in labarai dake yankin, Alhaji Sanusi Doro ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Guri a ranar Alhamis, inda ya ce wannan sharar cire ciyarwa da aka yi wani mataki ne wajen dakile aukuwar ambaliyar ruwa a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ciyarwar kachalla ciyawa ce da take rufe hanyar wucewar ruwa kuma tana tattara kwari masu hadarin gaske. Ya bayyana cewa; a gargajiyance aka cire ciyarwa saboda cukowar ruwa a cikinta ya hana a yi amfani da kayayyakin zamani wajen cire ta.

Ya tabbatar da cewa; aikin ya gudana ne a karkashin kulawar mashawarci na musamman kan harkokin yiwa al’umma aiki ga gwamna Badaru, wato Alhaji Hamza Mohammad-Hadejia.

Ya ci gaba da cewa; wadanda suka gudanar da aikin kungiyoyin matasa ne wadanda suka kware wajen cire irin wadannan ciyawar, inda suka bukaci gwamnati ta ba su naira dubu 180 a duk kilomita guda. Ya ce; ana tunanin ma’aikatan za su cire wannan ciyawar da ta kai akalla kilomita 35 a wani mataki na dakile ci gaba da ambaliyar ruwa a yankin.

Rahotanni sun ce; ya zuwa yanzu suna yankin Zoriyo, inda suke amfani da kananan kwale-kwale, igiyoyi da kuma wadansu kayayyaki da ake amfani da su a gonaki. Kamar yadda Doro ya tabbatar.

A karshe jami’in labaran, ya ce; akalla matasa 100 ne suke gudanar da aikin, inda ya ce matasan sun fito ne daga kauyukan Gajiya, Gajimaran, Dagana da Dabarmagini.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: