Connect with us

Uncategorized

Barazanar ‘Yan Aware A Kamaru Ta Tilastawa Jama’a Tserewa

Published

on

Rahotanni daga kasar Kamaru na nuni da cewa dubban al’ummar da ke yankin masu amfani da turancin Ingilishi na ci gaba da tserewa sakamakon barazanar ‘yan aware na ci gaba da kaddamar da hare-hare.

Wasu majiyoyi dai na bayyana cewa Mayakan ‘yan awaren masu fafutukar sun sha alwashin kaddamar da hare-hare a muhimman wurare da ke kasar ta Kamaru bayan hukuncin daurin rai da rai kan shugabanninsu.

A makon jiya ne dai wata kotun soja ta zartaswa shugabannin masu fafutukan awaren su 10 hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, matakin da masana ke ganin kaiya harzuka mayakan kungiyar ‘yan awaren.

Wani mazaunin yankin Muntari Hamisu ya tabbatarwa da sashen hausa na Radio France International rfi faruwan lamarin ya na mai cewa hatta kudin motar safara daga yankin zuwa sauran sassan kasar sai da ya yi tashin gwauron zabi.

A cewar Muntari Hamisu ficewar jama’a daga yankin ‘yan awaren na da nasaba da yadda suka dakatar da harkokin karatu bayan kulle ialhirin makarantun yankin, matakin da ya sanya iyayen da ke son ‘ya’yansu su samu karatu tserewa.

Rahotanni sun bayyana cewa al’ummar yankin da dama sun razana da barazanar ta ‘yan aware. A kamarun dai, Kimanin mutane 3 ne suka mutu kana wasu mutanen 7 suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kife a tekun Bakassi Peninsula dake kudu maso yammacin jamhuriyar Kamaru da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda jami’an tsaron tekun Kamaru suka bayyana.

Laftanal Kanal Emmanuel Sone, jami’i mai kula da tekun Kamaru ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Dinhua da yammacin ranar Litinin cewa, sun yi nasarar ceto mutane 107, sai dai abin takaici sun gano gawarwakin mutane 3 a wajen.

A cewar Laftanal Kanal Sone, mutane 117 ne a cikin kwale-kwalen, kuma mutane 7 din da suka bace wata kila sun makale ne a jikin jirgin ruwa. Wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta daga kamfanin jirgin ruwan Achouka ta tabbatarwa Dinhua adadin fasinjojin dake cikin jirgin ruwan.

To sai dai kuma, gidan talabijin na kasar Kamaru CRTB, ya sanar a yammacin Litinin cewa, fasinjoji 40 ne suka bace.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: