Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Binuwe: Ya Yi Wa Diyar Makwabcinsa ’Yar Shekara Uku Fyade

Published

on

Runduinar ‘yan sandar Jihar Benuwe ta cafke wani mutum mai shekaru da haihuwa, bisa yi wa diyar makwabcinsa mai shekaru uku fyade a karamar hukumar Gboko ta jihar. Shi dai wanda a ke zargi mai suna Kalu Agwu, dan kasuwa ne daga Juihar Abiya, amma mazaunin garin Gboko ne, ya danganta wannan mummunar aika-aika da ya aikata ga sherin shedan. An dai gurfanar da Agwu a sashen rundunar ‘yan sanda masu binciken manyen laifuka ta jihar da ke garin Makurdi, ya amsa laifinsa.

Ya bayyana wa manema labarai cewa, karamar yarinyar ta zo dakinshi sai ya fara wasa da ita, inda a nan ne sha’awa ya kai shi ga yin lalata da ita. Wanda a ke zargin ya yi kokarin rufe lamarin bayan ya aikata wannan mummunan aika-aika. Ya kara da cewa, ya na rokon iyayen yarinyar da su gafarce shi.

A halin yanzu dai, kakakin rundunar ‘yan sandar jihar DSP Catherine Anene, ya bayyana cewa, rundunarsa za ta tabbatar an gurfanar da wanda a ke zargi a gaban kuliya, sannan kuma ya shawarci da su dunga kulawa da ‘ya’yansu musamman ‘ya’ya mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!