Connect with us

KIWON LAFIYA

Gwamnatin Amurka Ta Sake Taimakon Nijeriya Da Dala Milyan 75

Published

on

Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta da matakin sake tallafawa Nijeriya da kudade dala miliyan 75 don yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids, wannan kuma a dai dai lokacin da masu fama da cutar ke ci gaba da barazanar yadata matukar hukumomi suka kasa samar masu da magungunan rage radadin kaifinta.

Cikin sanarwar da sashen samar da agajin gaggawa na cutar ta HIV Aids na fadar shugaban kasar Amurka PEPFAR ta fitar a jiya Talata, ya bayyana cewar kasar za ta karawa Nijeriyar agajin dala miliyan 75 don dakushe yadda irta cutar take kara karfi . Kamar dai yadda jakadan Amurkan a Nijeriya Stuart Symington kudaden dala miliyan 75 kari ne kan tallafin kasar ga Nijeriya don samar da magungunan rage kaifin cutar ta HIV Aids, dai dai lokacin da Nijeriyar ke fuskantar bore daga masu eauke da cutar sakamakon karancin magungunan ta.

Mr Stuart Symington ya ce Amurka za ta ci gaba da taimakawa Nijeriyar ta hanyar samar mata da kudaden magungunan rage kaifin cutar don rage radadi ga wadanda suke fama da cutar ta HIV Aids mai karya garkuwar jiki.

Matakin na Amurka dai na zuwa a dai dai lokacin da al’umma wadanda yawansu mata ne da kananan yara da ke dauke da cutar ta HIV Aids ke barazana ga gwamnati Nijeriyar sakamakon karanci baya ga tsadar magungunan rage kaifin cutar, inda ko a watannin da suka gabata , matan banza da suka kamu da cutar sun sha alwashin ci gaba da yada ta matukar ba a samar da magungunan rage kaifin cutar a saukake ba
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: