Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Legas: ’Yan Sanda Sun Cefke ’Yan Kungiyar Asiri 25

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta samu nasarar cafke ‘yan kungiyar asiri guda 25, a yankunan Ijora, Mushin da kuna Bariga da ke jihar tare kwato muyagun makamai. An bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda masu yaki da ayyukan kungiyar asiri ta cdamke wani mutum mai suna Olaitan Rilwan dan shekara 20 tare da wata karamar bindiga a cikin jakarsa.

A cikin bayanin kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Bala Elkana ya bayyana cewa, wandanda a ke zargin sun amsa laifinsu, inda su ka bayyana cewa su ‘yan kungiyar asiri ne ta Aiye Confraternity. Ya kara da cewa, an damke wasu ‘yan kungiyar asiri da kuma ‘yan fashi da makami a lokacin wannan sintiri.

Elkana ya ce, “a ranar 24 ga watan Agusta da misalin karfe hudu, tawagar ‘yan sanda su ka damke wani mutum mai suna Olaitan Rilwan dan shekara 20 tare da karamar bindiga a cikin jakarsa, a mahadar hanya da ke yankin Ijora. “Wanda a ke zargin ya bayyana cewa, shi dan kungiyar asiri ne ta Ayie Confraternity. An dai cafke wani mutum mai suna Mustapha Oseni dan shekara 23 da kuma wasu mutum 22 wadanda a ke zargi a yankin Bariga.”

A cewarsa, ‘yan sanda sun kuma damke wasu ‘yan fashi da makami tare da kwato muyagun makamai. Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda sashen masu yaki da ayyukan ‘yan kungiyar asiri wanda Sufeto Atipa Agasa ya ke jagoranta, sun kaddamar da sintiri na musamman a ranar 22 ga watan Agusta da misalin karfe 7.30 na safe, a tashar Olorunsogo da kuma yankin Mushin, inda su ka cafke wani mutum mai suna Matthew Omisogun dan shekara 25 da kuma Yetunde Lawson mai shekaru 28, a kan babur.

Ya ce, lokacin da wadanda a ke zargi su ka ga  tawagar ‘yan sanda, sai su ka yi kokarin gudu, amma sai dai ‘yan sanda sun samu nasarar damke su. Ya kara da cewa, an kwato karamar bindiga kirar gida guda daya tare da harsashi guda biyu daga hannunsu. Elkana ya cigaba da cewa, wadanda a ke zargin su na cikin tawagar ‘yan fashi da makami guda biyar, wadanda su ka addabi yankunan Mushin, Ikotun da kuma Igando da ke cikin jihar.

Ya ce, an mika wadanda a ke zargin zuwa sashe rundunar ‘yan sanda masu yaki da ayyukan ‘yan fashi da makami, domin gudanar da cikakken bincike. Ya ce, an bada jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!