Connect with us

RA'AYINMU

Batun Aiki Kafada Da Kafada A Tsakanin Hukumomin Tsaro

Published

on

Tun bayan zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, Gwamnatinsa ta dauki tsauraran matakai wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda. Kazalika, an samu nasarori iri daban-daban wajen yaki da wannan ta’addanci da kuma kashe-kashen wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk dai da cewa; ta’adancin ya sake sauya salo mai matukar daukar hankali.

Wannan ta’addanci da kai harehare da wadannan ‘yan ta’adda da sauran masu kashe-kashen mutane ke yi, musamman a yankunan Arewa maso gabas da kuma Arewa maso yamma, an dora alhakin ne a kan rashin jituwa da fahimtar juna tsakanin Jami’an tsaro, ma’ana Sojiji da ‘Yan Sanda da kuma sauran Jami’an tsaron farar hula da fari kaya.

Babban abin da ya tabbatar da haka kuwa shi ne, babu cikakken hadin kai tare da karfafar juna wajen aiwatar da aiki a tsakanin wadannan Jami’an tsaro. Wannan ne yasa ake samun rahotanni masu cin karo da juna, kowane bangare na wadannan Jami’an tsaro na bayar da nasa daban.

Babu shakka hakan, yasa an koma kallon Nijeriya a matsayin wadda ba ta taimakon kanta a bangaren sha’anin Jami’an tsaronta, da ta kai ta kawo har gwabzawa suke yi a gaban jama’a, tare da yin musayar yawu a kafafen hada labarai.

Haka zalika, har sai da ta-kaita-kawo wasu Jami’an tsaro sun cafke wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, wasu Jami’an tsaron daban kuma sun kubutar da su ta karfin tsiya, wanda wannan har ma za a rasa yadda za a siffanta ko bayyana al’amarin.

Har ila yau, babban abin haushi da takaici shi ne, yadda wadannan Jami’an tsaro ke cin dunduniyar kawunansu da zarge-zargen junansu tare da hadin baki wajen far ma junansu da kuma kashe kawunansu.

Kamar dai abin da ya faru a kwana-kwanan nan na kisan ‘Yan Sanda guda uku da kuma wasu mutane guda biyu da Sojoji suka yi. Haka nan, babu jimawa ‘Yan Sanda sun cafke wani kasurgumin mai yin garkuwa da mutane, Bala Hamisu (Aka Wadume), a Jihar Taraba; wanda a karshe ta karfin tsiya Sojoji suka tseratar da shi tare da yin kisan kai.

Duk dai da cewa, ‘Yan Sanda sun sake cafke Wadume, amma dai Sojoji na da hannu dumu-dumu wajen tseratar da shi, tare da kashe manyan Jami’an na ‘Yan sanda wanda hakan ke bukatar bincike mai zurfin gaske. Kazalika, ‘Yan Sanda, sun fitar da wani faifan bidiyo da yake ta faman zagaya wa a kafafen sada zumunta, wanda shi da kansa Wadume ke tabbatar da cewa, Sojoji ne suka kubutar da shi daga hannunsu har ya samu ya gudu.

Kodayake, su ma a nasu bangaren, Sojojin sun musunta hakan tare da cewa, babu yadda za a yi kawai a yi la’akari da bangare guda ba tare da an ji daga dayan bangaren ba, sannan sun kalubanci kasancewa cikin wadanda za su zamto ana zargi ko tuhuma wajen aikata ta’addanci da sauran makamantansu.

Duba da yadda wannan al’amari ya faru, ya kyautu idan ‘Yan Sanda suka gabatar da wannan fefan bidiyo ga wadanda za su yi binciken kwakwaf a kansa, su tsaya su bi diddigin al’amarin yadda ya kamata don gano gaskiyar abin day a faru.

Dalili kuwa, Jami’an ‘Yan Sanda za su iya yin komai cikin fushi da bacin rai, musamman ganin yadda suka rasa wasu daga manyan kwararrun Jami’ansu da suke ji da su. Har wa yau, akwai darasi da dama da kyautu a ce an koya daga ire-iren wadannan abubuwa da suka faru a tsakanin wadannan Jami’ai na tsaro. Don haka, muna kira da Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta yi kokarin tsayawa iya matsayinta na baiwa Jami’an ‘Yan Sanda dukkani irin bayanan sirrin da suka dace. Wani abu day a faru kwanan nan na cafke wasu da Jami’an tsaron farin kayan suka yi (DSS), ya yi matukar daukar hankalin al’ummar wannan kasa.

Abin mamaki, a lokacin da Jami’an ‘Yan Sanda ke tuhumar wadanda ake zargi da aikata laifuka, a daidai wannan lokaci sai ga shi su ma Jami’an hukuma ta farin kaya (DSS), na tuhumar wadannan masu laifi, Jami’an na DSS sun kai wadanda ake zargin wannan Kotu, su kuma ‘Yan Sanda sun kai su wata Kotu daban a kan kuma laifi iri guda.

Don haka, kamata ya yi Jami’an Hukuma na farin kaya, su rika aiwatar da ayyukansu cikin sirri tare da yin bincike suna tattara bayanai suna tura wa Jami’an Sanda wadanda su ne ke da alhakin kamo wadanda ake zargi da aikata laifuka, sannan su tura su Kotu bayan su ma sun kammala nasu binciken.

Haka nan, su ma Jami’an Hukumar ‘Yan Sanda, ya kamata su rika baiwa sauran Jami’an tsaro karfin gwaiwa, tare da amincewa da su.

A duk lokacin da aka kawo musu masu laifi, su tabbata sun yi abin day a kamata, ba kawai su rika karbar kudi suna rabuwa da su ko sakinsu; suna zuwa suna cigaba da aikata miyagun laifuka ba, ko kadan wannan ba zai taba Haifa wa wannan kasa da mai ido ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!