Connect with us

BABBAN BANGO

Bikin Baje Kolin Lambunan Shakatawa Na Beijing 2019 Babbar Dama Ce Ta Inganta Muhallin Kasashe Masu Tasowa

Published

on

Masu hikimar magana na cewa na zaune bai ga gari ba, a ranar 29 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2019 ne aka kaddamar da kasaitaccen bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bikin wanda za a shafe tsawon kwanaki 162 ana gudanar dashi wato kusan rabin shekara kenan. Bikin ya samu halartar kasashen duniya 86, da kungiyoyin kasa da kasa 24, da ma sauran sassan da bana gwamnati ba 120 sun samu halartar bikin a wannan karo. Shi dai bikin baje kolin lambunan shakatawar ya shafi dukkan nau’ikan shuke shuke da furanni da nau’in kayan amfanin gona da bishiyoyi da dai sauransu, wadanda ke tallafawa jin dadin rayuwar dan adam, da baiwa muhalli kariya, da kyautata yanayin muhalli, da kuma kawatashi yadda ya kamata. Wasu da dama daga cikin mahalarta bikin wadanda na zanta dasu sun bayyana cewa, bikin ya zamto tamkar wani muhimmin dandali ne na yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta fannin bunkasa harkokin kiyaye muhalli, kyautata muhallin sauran halittu, samar da kandagarkin kwararowar hamada, da kuma samar da ni’imtattun wurare ga dubun dubatar masu sha’awar yawon bude ido a sassa daban daban na duniya

Masu iya magana kance gani-ya-kori-ji, a hakika bisa ziyarar da na kai domin ganewa idona yadda aka shirya wannan muhimmin bikin, abin sai wanda ya gani, tabbas bikin yayi matukar kayatar dani da ma dunbun jama’a daga sassa daban daban na duniya musamman bisa yadda aka kwashe tsawon lokaci wajen shirye shiryen da suka dace da kayata wajen don biyan muradun mahalarta bikin.

Alal hakika, wannan mashahurin biki na baje koli ya ja hankalin kasa da kasa domin kuwa ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatarsa kasancewar bikin yana gudana ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar matsalolin sauyin yanayi wanda ke shafar muhallin da dan adama ke rayuwa cikinsa har ma da muhallin sauran hallitu lamarin da ke kara barazanar bacewar wasu nau’ikan hallitu daga doron kasa. Ziyarar da na kai wannan yankin dake wajen birnin Beijing na kasar Sin inda aka tanada saboda wannan biki na musamman, ya samu halartar kasashe masu yawa daga dukkan nahiyoyin duniya kama daga nahiyar Asiya, Turai, Afrika, yankin gabas ta tsakiya da sauran sassan duniya baki daya. A bisa al’adar bikin baje kolin, akan ware rana guda sukutun ga kowace kasa ko yankin wanda ya kafa rumfarsa a wajen bikin baje kolin domin su samu damar gudanar da shagulgula na musamman wanda ya kunshi jawabai daga jami’an jakadancin kasar, gami da gudanar da nune nunen al’adun gargajiya da suka hada da kade kade da raye raye na wannan kasa ko yankin domin su kara fito da al’adun gargajiyar kasar ko yankin da nufin tallatawa duniya. A wannan rana na kai ziyarar ne musamman domin halartar bikin ranar jamhuriyar Nijer, wanda ya gudana a ranar 4 ga watan Agusta

Bikin ya samu halartar baki da dama daga kasashen duniya, ciki har da wasu jakadun kasashen Afrika, da wasu jami’an gwamnatin kasar Sin, gami da sauran alummar Sinawa da na wasu kasashen Afrika da dama. An gudanar da kade-kade da raye-raye na gargajiya daga wasu shahararrun mawakan jamhuriyar Nijer.

Jakadan Nijer a kasar Sin,Inoussa Moustapha, ya halarci bikin tare da gabatar da muhimmin jawabi. A cikin jawabinsa ya bayyana cewa, halartar bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa da Nijer ta yi a wannan karo ya shaida muhimmancin da gwamnatin kasar ta dora ta fannin raya ayyukan gona da ma kiyaye muhalli, da kuma yadda gwamnati ke mayar da hankali kan samar da isasshen abinci da nau’in abincin mai gina jiki ga al’ummar kasar. Ya kara da cewa, kasar Sin ta gabatar da manyan gyare-gyare ga tattalin arzikinta, kuma ta samu babban ci gaba ta fannin saukaka fatara da raya zamantakewar al’umma, abinda ya baiwa kasashen Afrika matukar kwarin gwiwar kara amincewa da kasar Sin don yin hadin gwiwa a dukkan fannoni. Ya ce kasar Sin tana taimakawa kasashe masu tasowa wajen saukaka fatara da raya karkara, don haka ya yi amanna hadin gwiwar bangarorin biyu zai tabbatar da ci gaba mai ma’ana.

Malam Yacouba Souley, daya daga cikin ma’aikatan dake kula da rumfar jamhuriyar Nijer, ya gabatar mini wasu daga cikin muhimman kayayyakin da aka yi baje kolinsu a rumfar ta Nijer, ya kuma bayyana farin cikinsa game da wannan rana ta jamhuriyar Nijer da aka yi bikinta.

Taken bikin baje kolin na wannan karo shi ne “kiyaye muhalli, rayuwa mai inganci”.

Akwai kasashen Afirka da dama da suka halarci wannan bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na Beijing, akwai wani bangaren da aka kebe musamman na rumfunan kasashen yammacin Afirka, ciki har da kasashen Ghana, da Benin, da Senegal, da Mali, Mauritania da dai sauransu. Haka zalika, na samu damar zagaya rumfunan, kuma a rumfar Ghana, na ga kayayyaki iri iri da aka baje kolinsu, ciki har da nau’o’in furanni, da shuke-shuke, da riguna da kayayyakin ado, da zane-zane, da kayayyakin sassaka da makamantansu, wadanda ake samar dasu a kasar Ghana.

A rumfar ta Ghana, na kuma samu damar tattaunawa da wani ma’aikaci mai kula da rumfar, Laurence Yand, inda ya yi mini karin haske game da irin kayayyakin da kasarsa tayi baje kolinsu a rumfar, ya ce, Ghana ta baje kolin kayayyaki masu yawan gaske, akwai kayayyaki na bishiyar koko Ghana tana daya daga cikin kasashen da suka fi samar da koko a duniya baki daya, sun gabatar da nau’in kayayyakin da ake samarwa daga koko, ya kara da cewa, kayayyakin sun samu karbuwa a wurin masu ziyara. Sannan al’ummar Sinawa dake kawo ziyara a rumfar Ghana suna sha’awar kayayyakin, suna sayensu, da zarar sun dandana suna sonsu sosai kuma suna sayensu.

Laurence yace, bikin baje kolin ya tattara kasashe daban daban na duniya zuwa waje guda, zaka iya yin cudanya da al’adun mutanen kasashe daban daban, wannan babbar dama ce ta yin mu’amalar cinikayya da mutane na kasashen duniya.

Akwai wata bishiya da aka nuna a rumfar Benin wato zogala wacce a turance ake kira Moringa. Ance wannan bishiyar tana da dubun amfani mai yawa ga rayuwar bil adama wajen samar da abinci mai gina jiki baya ga magunguna da ake samu daga bishiyar ta zogala, kamar yadda wani jami’i mai kula da rumfar kasar Benin, Virgile Ahouamdjinou, ya bayyana mini. Yace jamhuriyar Benin ta gabatar da zogale a wannan bikin baje kolin, wato nau’in bishiya ce mai abin al’ajabi bishiyar tana maganin cututtuka sama da 300, wannan ne dalilin da yasa kasarsa ta gabatar da wannan bishiyar a wajen bikin bajekolin tare da fatan zata amfanawa al’ummar sinawa har ma da sauran alummar kasa da kasa.

A rumfar Senegal, na hadu da malam Boubacar Diouf, jami’in da ke kula da rumfar, ya kuma bayyana manufar da Senegal ke neman cimmawa a wannan bikin baje kolin, ya ce, bikin bajekolin lambunan shakatawa wanda ya shafi dukkan nau’ikan tsirrai, da furanni da shuke shuke, wannan ne dalilin da yasa gwamnatin Senegal ta dauki batun da matukar muhimmanci inda ta dauki matakan inganta dukkan wuraren da mutane ke ziyarta domin tabbatar da ingancin muhalli. Manufa ta biyu itace, kasar Senegal tana son bayyanawa duniya irin abubuwan da take yi a fannin kyautata yanayin lambunan shakatawa kamar yadda akwai nau’ikan kayayyaki masu yawa a cikin rumfar kasar ta Senegal akwai abubuwa masu yawa na kasar wadanda suka shafi lambunan shakatawa kuma akwai furanni iri iri, da wasu nau’in tsirrai da ganyaye da ake hada magunguna da su, wannan shine dalilin da yasa suka zo domin halartar wannan bikin baje koli na Beijing. Har wa yau, malamin ya ce akwai makoma mai kyau ta bangaren aiwatar da hadin gwiwar kiyaye muhalli a tsakanin Senegal da kasar Sin.

Hakika, wannan kasaitaccen bikin bajekolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na Beijing 2019, wata muhimmiyar dama ce ta kara zurfafa hadin gwiwar Sin da sauran kasashen duniya ta fannin kyautata muhalli da inganta yanayin zaman rayuwar bil adama da samar da launin kore, da kawata wurare, da kuma samar da ni’imtattun wuraren yawon shakawa ga dan adama domin kyautata jin dadin rayuwar dukkan bil adama da fatan alummar duniya musamman kasashen masu tasowa daga nahiyar Afrika zasu tsaya tsayin daka wajen kare muhalli da kyautatashi. Ahmad Inuwa Fagam, daga shashen Hausa na gidan radiyon kasar Sin, Beijing, China.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: