Connect with us

LABARAI

Boko Haram: Sojojin Nijeriya Sun Tattauna Da Kungiyar Dattawan Borno

Published

on

Rundunar Sojojin Nijeriya ta yi wata ganawa da Kungiyar Dattawan jihar Borno sakamakon damuwa da al’umma ke nunawa kan sabunta hare-hare da Boko Haram ke yi a jihar, abin da ya haifar da tsoro da kuma tserewar wasu al’ummomi daga garuruwan su. Rahotanni daga jihar Borno sun bayyana cewa; sojojin sun yi ganawar ne a asirce, inda bayan fitowarsu suka yiwa manema labarai karin bayani.

Birgediya Janar Abdul Khalifa Ibrahim, wanda shi ne babban Kwamandan runduna ta uku da ke yaki da Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Nijeriya, ya yi karin haske kan sabuwar dabarar yaki da suka fito da shi. Inda ya ce suna samun matsala ne da Boko Haram, amma yanzu za su canza fasalin dabarar yakin. Ya ce za su dauki dabarar abin da ake cewa ‘Super Camp’, za su yi amfani da wannan dabarun wajen ganin sun cimma nasarar murkushe Boko Haram din.

Wasu bayanai sun nuna cewa; wannan ganawar ya biyo bayan korafin da kungiyar Dattawan Borno din suka rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da koma bayan da ake samu a yaki da Boko Haram a yankin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!