Connect with us

Da dimi-diminsa

Gwamnan Bauchi Ya Tsige Mai Bashi Shawara Kan Harkokin Siyasa

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya sallami babban mai bashi shawara na musamman kan harkokin Siyasa, Alhaji Musa Haruna Shittu.

Wannan sallamar tana zuwa ne watanni kalilan da nada shi wannan mukamin.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Ladan Salihu ya sanya wa hannu a yau Jumma’a, ya shaida cewar Gwamnan ya dakatar da Shittu ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba.

Gwamna Bala ya gode wa mai bashi shawara kan harkokin siyasan a bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar ta Bauchi.

Ga abun da sanarwar ke cewa, “Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya amince da dakatar da Alhaji Musa Haruna Shittu a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin siyasa.

“Wannan dakatarwar ta fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba,”

“Gwamna ya gode wa tsohon mai bashi shawara kan harkokin siyasar a bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar, ya kuma masa fata mai kyau a rayuwarsa ta gaba,” A fadin sanarwar.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace hakikin dalilin daukar wanna matakin ba. A bisa haka, wakilinmu ya tuntubi korarren mai bada shawarar amma ya ki daukar wayar, kana ya aike masa da sakon kar ta kwana shiru don jin ta bakinsa.

Wanna matakin dai na zuwa ne bayan wasu ‘yan watanni kadan da bashi wannan mukamin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: