Connect with us

WASANNI

Messi Ya Sake Jin Ciwo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zata sake buga wasan laliga na sati na uku ba tare da dan wasanta Leonel Messi ba bayan da wasu rahotanni suka bayyana cewa dan wasan ya sake jin ciwo a filin daukar horon kungiyar.

Tun bayan da aka fara wasannin share fage domin tun karar kakar wasan wannan shekarar Messi dai bai fara bugawa Barcelona wasa ba saboda ciwon daya samu a gasar cin kofin Copa America da aka fafata kuma bai bugawa kungiyar wasanni biyun data buga ba a baya da suka buga da Atletico Bilbao da Real Betis.

Sai dan anyi zaton dan wasan zai samu damar buga wasan da kungiyar zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Osasuna a ranar Asabar amma kawo yanzu ana shakkun ko zai iya buga wasan ko bazai buga ba.
Wani rahoto da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa dan wasan bai sake jin ciwo ba kuma yana cigaba da samun sauki amma kuma duk da haka bai samu damar daukar horo ba a ranar Alhamis din data gabata kamar yadda wani rahoto ya tabbatar.

A ranar 7 ga watan gobe za’a fara buga wasannin kasashe hakan yana nufin babu wasannin kungiyoyi saboda haka kociyan kungiyar bazaiyi gangancin saka dan wasan ba har sai an dawo daga hutu. Banda Messi shima dan wasan gaba na kungiyar, Luis Suares baya bugawa kungiyar wasa saboda ciwon daya samu yayinda shima Ousmane Dembele shine yake jinya saboda raunin daya samu a wasan kungiyar na farko.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: